Damilola Adegbite | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Lagos,, 18 Mayu 1985 (39 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Mazauni | Lagos, |
Harshen uwa | Yarbanci |
Ƴan uwa | |
Abokiyar zama | Chris Attoh (2015 - 2017) |
Karatu | |
Makaranta |
Jami'ar Bowen Queen's College, Lagos |
Matakin karatu | Digiri |
Harsuna |
Turanci Yarbanci Pidgin na Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | jarumi da model (en) |
IMDb | nm5270569 |
Damilola Adegbite (an haife ta a Oluwadamilola Adegbite; 18 Mayu, 1985) 'yar wasan kwaikwayo ce ta Nijeriya, Tauraruwa, kuma sananna a shirye-shiryen Talabijin.[1] Ta taka rawa a matsayin Thelema Duke a shirin Tinsel, ta kuma fito a matsayin Kemi Williams a fim din Flower girl.[2] Ta lashe kyautar Gwarzuwar Jaruma (Best Actress) a shirin Talabijin a shekara ta 2011 a gasar Nigerian Entertainment Award.[3]
An haifeta a garin Surulere, jihar Legas. Ta halarci makarantar Queens College dake Yaba, Legas sannan ta karanci harkokin kasuwanci (Business Administration) a Jami’ar Bowen da ke Iwo, Jihar Osun. Tinsel shine shirinta na farko a wasan kwaikwayo.[4] Ta kuma bayyana a cikin tallan TV da shirye-shiryen da aka gabatar a talabijin.[5]
A watan Agusta 2014, Adegbite tayi aure da Chris Attoh, wani dan wasan fim din da ta hadu da shi a fim din Tinsel na opera.[6] A watan Satumba na 2014, ma'auratan sun samu ḱaruwa ɗa namiji Brian.[7] Adegbite da Attoh sun yi aure na sirri a Accra, Ghana a ranar 14 ga Fabrairu, 2015.[8] A watan Satumba na 2017, labari ya bazu cewa auren Adegbite da mijinta Chris Attoh ya lalace. Adegbite ta haifar da yaduwar jita-jitan bayan ta goge sunan Chris Attoh daga jikin sunanta a asusun ta na sada zumunta. Sannan ta dena biy-biyanshi a shafinta na Instagram, ta goge duk hotunan sa daga asusun ta na sada zumunta.[9] Sa’o’i bayan haka, a zantawa da akayi da Chris Attoh ya tabbatar da cewa aurensa da Damilola Adegbite ya mutu.[10][11]