Daniel Etim Effiong | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Jahar Kaduna, |
ƙasa | Najeriya |
Karatu | |
Makaranta |
Federal University of Technology, Minna Digiri a kimiyya : chemical engineering (en) Jami'ar Johannesburg |
Matakin karatu | Digiri |
Harsuna | Turanci |
Sana'a | |
Sana'a | jarumi, darakta, chemical engineer (en) da marubin wasannin kwaykwayo |
IMDb | nm5652097 |
Daniel Etim Effiong, kuma Daniel Etim-Effiong[1] ɗan wasan Nollywood ne na Najeriya kuma darektan fina-finai.[2]
An haife shi a Jaji, jihar Kaduna a Najeriya kuma ya rayu a birnin Benin na jihar Edo ; Jihar Legas da Abuja. Mahaifinsa yana cikin sojojin Najeriya.[3] Mahaifinsa, Laftanar Kanar Moses Effiong ya samu afuwa a hukumance daga shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da wasu mutane biyar da aka yankewa hukuncin ɗaurin rai-da-rai a shekarar 1986, bayan da aka zarge shi da yin juyin mulki na mai taken, 'Vatsa' a lokacin mulkin Ibrahim Babangida, bisa zarginsa da laifin ɓoyewa gwamnatin ƙasar da cin amanar ƙasa, wanda aka saki a shekarar 1993 amma ba tare da shela a hukumance da maido masa da muƙamin sa da hakki ba.[4]
Ya halarci makarantar St. Mary's Private School, Legas Island, Legas sannan ya ci gaba da karatunsa na sakandare a Kwalejin Gwamnati, Ikorodu, Legas. Daga nan sai ya wuce Jami'ar Fasaha ta Tarayya da ke Minna ta Jihar Neja, inda ya yi karatun digiri na farko a fannin injiniyan sinadarai. Bayan wani ɗan takaitaccen lokaci na aiki a masana’antar man fetur da iskar gas a matsayin injiniya, ya yanke shawarar sauya sana’a sannan ya ci gaba da karatun harkar fim, rubutu da bayar da umarni a Makarantar Fina-Finai ta AFDA da ke kasar Afirka ta Kudu sannan ya yi kwas a Jami'ar Johannesburg kan shirya fina-finai.[3]
Bayan ya bar aikin mai da iskar gas, ya zama mai shirya wasu tsare-tsare ga NdaniTV.[5]
A cikin 2017, ya shirya wani gajeren fim mai tsawon minti biyar mai suna, " Prey ", wanda amaryarsa, Toyosi ta shirya, tare da Tope Tedela da kuma Odenike Odetola.[6]
Bland2Glam ta nuna shi a cikin 2019 a lokacin kamfen ɗinta na #ThePowerof7 don bikin shekara bakwai a masana'antar, fashion industry.[7]
Ya fito tare da 'yan wasan kwaikwayo na Kenya Sarah Hassan da Catherine Kamau Karanja a cikin fim ɗin barkwanci na shekarar 2019, mai suna Plan B inda ya taka rawar a matsayin Dele Coker, shugaban Najeriya na wani kamfani da ke Nairobi.[8][9][10][11] A dalilin Fim ɗin ya sami lambar yabo ta Mafi kyawun ɗan wasan kwaikwayo a cikin shirin barkwanci (Fim / TV Series) a cikin jerin lambobin yabon da aka bayar na AMVCA karo na 7, da aka bayar a shekarar 2020.[5]
Ya fito a cikin fina-finai da yawa da akayi a shekara ta 2020. Ya taka rawar gani a fim din " Fish Bone ", wanda Editi Effiong ya shirya shi ma Shaffy Bello da Moshood Fattah.[12] An nuna shi tare da Ike Onyema da Atteh 'SirDee' Daniel a cikin gajeren fim ɗin, " Storm ", wanda Diane Russet ya shirya kuma Michael 'AMA Psalmist' Akinrogunde ya ba da umarni.[13][14] Har yanzu a cikin 2020, ya ba da umarnin wani shirin gaskiya mai taken, " Skin ", wanda Beverly Naya ya shirya.[15][16] An tsara shi don nunawa akan dandalin kallo a yanar gizo wato NETFLIX.[17]
Shekara | Suna | Matsayi | Bayani | Madogara |
---|---|---|---|---|
2019 | Castle and Castle | Mike Amenechi | [18] | |
2018- | The Men’s Club | Lanre | [19] | |
2013 | Gidi Up | Folarin | [19] | |
2021 | Castle & Castle | Mike Amenechi | [20] | |
2022 | Blood Sisters |
Shekara | Suna | Matsayi | Bayani | Madogara |
---|---|---|---|---|
2022 | Kofa | Wale | Earned AFRIFF award and AMVCA nomination | [21] |
2021 | Still Falling | Captain Lagi | Alongside Sharon Ooja | [22] |
2020 | Skin | Director | Documentary Featuring Eku Edewor and Beverly Naya | [23] |
2020 | Storm | Storm | Short film alongside Diane Russet | [24] |
2020 | Fish Bone | Inspector | Shortfilm alongside Shafy Bello and Moshood Fattah | [25] |
2019 | Òlòtūré | Tony | [26] | |
2019 | Makate Must Sell | |||
2019 | Plan B | Dele Coker | Lead role | [27] |
2018 | New Money | Ganiyu Osamede | [28] | |
2017 | Prey | Director | Short skit | [25] |
Shekara | Kyauta | Iri | Fim | Sakamako | Madogara |
---|---|---|---|---|---|
2022 | Africa International Film Festival | Best Actor In A Drama, Movie Or TV Series | Kofa | Lashewa | [21] |
2023 | Africa Magic Viewers' Choice Awards | Best Actor In A Comedy Drama, Movie Or TV Series | Ayyanawa | [29][30] |
Effiong ya auri Toyosi Etim-Effiong tun ranar 4 ga Nuwamba, 2017. Sun fara arba-(haduwa) ne a watan Agustan 2016 yayin gudanar da wani aiki.[31][32] Ma'auratan sun yi maraba da ɗansu na fari, mace a watan Janairu 2019.[33]