David Nii Addy (An haife shi a ranar 21 ga Fabrairun shekarata 1990) shi ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne a ƙasar Ghana, wanda ke taka leda a ƙungiyar Ilves da Ghana. An haife shi a Prampram.
Addy ya samu kiran Black Satellites na farko bayan da ya yi rawar gani tare da Local Black Stars a shekarar 2008, wanda ya fara zama na farko a watan Janairun shekarar 2008 a wasa da Angola. A shekara ta 2009 Addy yana daga cikin tawagar da ta lashe Gasar Matasan Afirka ta shekarar 2009 . Nasarar sa ta ci gaba a watan Oktobar shekarar 2009 yayin da shi ma ya halarci Gasar cin Kofin Duniya ta FIFA U-20 da aka gudanar a Misira wanda kungiyar ta ci gaba da lashe, wanda ya sa suka zama Kasar Afrika ta farko da ta taba cin Kofin Duniya na U-20 na shekarar 2009 .
An kira shi don Black Stars don wasa tare da Lesotho a ranar 8 Yuni 2008. [1] Wasansa na biyu shi ne ranar 2 ga Nuwamba 2008 da Nijar . An gayyaci Addy don ya bugawa kungiyar kwallon kafa ta kasar Ghana.
A shekara ta 2010, Addy ya auri wata Bajamusiyar Gana wadda ta karanci ilimin tattalin arziki. Ma'auratan sun fara haduwa a cikin shekarar 2008 a matsayin manyan abokan juna. A watan Mayu na 2014 Addy da matarsa suka yi bikin haihuwar ɗansu na fari. Ma'auratan sun kuma yin maraba da wata yarinyar da suka sake haifa a lokacin da suka koma rayuwa a Reading, Berkshire. [2]