![]() | |
---|---|
![]() | |
Rayuwa | |
Haihuwa | Ile Ife, 23 Nuwamba, 1961 (63 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Karatu | |
Makaranta |
Jami'ar Ibadan Bachelor of Arts (en) ![]() ![]() |
Harsuna |
Turanci Yarbanci |
Sana'a | |
Sana'a |
jarumi, darakta, mai tsara fim da film screenwriter (en) ![]() |
Kyaututtuka | |
IMDb | nm2102029 |
Dele Odule (an haife shi a 23 ga watan Nuwamba, 1961) ɗan wasan fina-finan Najeriya ne kuma furodusa.[1] An zabe shi a cikin "Best Supporting Actor ( Yoruba )" a 2014 Best of Nollywood Awards saboda rawar da ya taka a fim din Kori Koto.[2] A halin yanzu yana aiki a matsayin shugaban kungiyar masu fasahar fina-finai da wasan kwaikwayo ta Najeriya wato Arts and Movie Practitioners Association of Nigeria.[3]
An haifi Odule a garin Oru Ijebu, cikin karamar hukumar Ijebu ta Arewa ta jihar Ogun a shekarar 1961,[4] inda ya yi karatunsa na farko da na sakandare. Ya mallaki takardar shedar Grade II daga Kwalejin Horar da Malamai ta Oru kafin ya wuce Jami'ar Ibadan ta Jihar Oyo[5] inda ya karanta fannin wasan kwaikwayo.[6]
Dele ya fara wasan kwaikwayo ne daga wata kungiyar wasan kwaikwayo mai suna Oloko Theater Group karkashin jagorancin Mukaila Adebisi. Ya fito a karon farko a shekarar 1986 kafin a haska bayan ya fito a fim din mai suna Ti Oluwa Ni Ile . Tun daga nan ya ci gaba da taka rawa a fina-finai sama da 200. [6]
Shekara | Bikin bayar da kyaututtuka | Kyauta | Sakamako | Ref |
---|---|---|---|---|
2014 | 2014 Best of Nollywood Awards | Best Supporting Actor (Yoruba) | Ayyanawa | |
2014 Yoruba Movie Academy Awards | ||||
2020 | Best of Nollywood Awards | Best Supporting Actor –Yoruba | Ayyanawa |