![]() | |||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
![]() | |||||||||||||||||||||||
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||
Haihuwa | Rotterdam, 4 ga Yuli, 1999 (25 shekaru) | ||||||||||||||||||||||
ƙasa |
Kingdom of the Netherlands (en) ![]() | ||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||
Muƙami ko ƙwarewa | Mai buga tsakiya | ||||||||||||||||||||||
Nauyi | 72 kg |
Deoy Duarte (an haife shi a ranar hudu 4 ga watan Yuli shekarar alif dubu daya da dari tara da casa'in da tara 1999) ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne wanda ke taka leda a matsayin ɗan wasan tsakiya a kulob ɗin Fortuna Sittard a cikin Dutch Eredivisie.[1] An haife shi a cikin Netherlands, yana wakiltar tawagar kasar Cape Verde.
Ya yi wasansa na farko na Eredivisie a kulob ɗin Sparta Rotterdam a ranar goma sha biyu 12 ga watan Agusta shekarar alif dubu biyu da goma sha bakwai 2017 a wasan da VVV-Venlo. [2]
A ranar goma sha biyu 12 ga watan Agusta shekarar alif dubu biyu da ashirin da daya 2021, ya sanya hannu kan kwangilar shekaru uku tare da Fortuna Sittard. [3]
An haife shi a Netherlands, Duarte dan asalin Cape Verde ne. An kira shi don ya wakilci tawagar kasar Cape Verde don wasan sada zumunci a cikin watan Maris shekarar alif dubu biyu da ashirin da biyu 2022.[4] Ya yi wasan sa na farko a Cape Verde a wasan sada zumunci da suka doke Guadeloupe da ci biyu da nema 2-0.[5]
Kani ne ga Laros Duarte.[6]