Djamila Sahraoui | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Tazmalt (en) , 1950 (73/74 shekaru) |
ƙasa | Aljeriya |
Karatu | |
Makaranta | Institut des hautes études cinématographiques (en) |
Harsuna | Faransanci |
Sana'a | |
Sana'a | darakta, jarumi da marubin wasannin kwaykwayo |
IMDb | nm0756389 |
Djamila Sahraoui (An haife ta a shekara ta 1950) yar wasan fina-finan Aljeriya ce.
An haifi Djamila Sahraoui a Algiers a ranar 23 ga watan Oktoba 1950. Ta yi karatun adabi kafin ta halarci fitacciyar makarantar fina-finai ta Paris IDHEC (Institut des hautes études cinématographiques), ta kware a rubuce-rubuce da shugabanci. Sahraoui ta koma Faransa a shekarar 1975 inda ta fara aikinta a matsayin mai shirya fina-finai. Ta yi gajeren fim ɗin ta na farko, Houria a cikin shekarar 1980, sannan ta yi aiki a matsayin edita kuma mataimaki, kafin ta ci gaba da yin nata shirye-shiryen daga shekarar 1990s. [1] Shirinta na 1995, La moitié du ciel d'Allah, ya gabatar da hirarraki da matan Aljeriya game da aiki da gwagwarmayar su na samar da daidaito da 'yanci. A cikin shekarar 1997, an ba ta lambar yabo ta la Villa Medicis saboda nasarar da ta samu.[2] Yayin da aka fi sanin Sahraoui da shirin fina-finanta, ta kuma samu nasara da fina-finan ta na almara Barakat! (2006) da Yema (2013).[3]