Doka Akan Namun daji | |
---|---|
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na | Doka |
Facet of (en) | farauta |
Dokan ƙayyade kamun Naman daji wasu ƙa'idoji ne waɗanda ke tsara ƴancin farautar ko kama, kashe wasu nau'ikan kifaye da namun daji ( Namun daji ). [1]An ƙayyade wasu daga cikin waɗan su iyakoki akan namun daji, Abubuwan da aka ƙayyade su na iya haɗawa da abubuwa masu zuwa: Ƙayyade kwanakin kamun kifi ko nama zai iya amfani dashi a wani lokaci, taƙaita adadin dabbobin da kowane mutum zai iya kamawa, taƙaita nau'in mutun farauta, da iyakance makamai da kayan kamun kifi da ake amfani da su ko yin farauta.Mafarauta, masunta da ƴan mahukunta gaba ɗaya sun yarda cewa makasudin irin waɗannan dokokin shine a daidaita buƙatun kiyayewa da da kuma kamun da sarrafa yanayi da yawan kifi da namun daji. Dokokin za su iya ba da tsarin doka mai kyau don tattara kuɗin lasisi da sauran kuɗi waɗanda ake amfani da su don tallafawa ƙoƙarin kiyaye namun daji tare da samun bayanan kamun shi da aka yi amfani da su a aikin sarrafa namun daji.[2][3]
A Burtaniya dokokin gandun daji sun samo asali daga dokokin gandun dazuka, wanda a zamanin sarakunan Norman waɗanda kasance masu zalunci. A ƙarƙashin William, babban laifi ne kashe ɗaya daga cikin barewa na sarki kamar kashe ɗaya daga cikin talakawansa. Wani matsayi da tsayin daka, ko mallakar wani adadi, sun kasance na dogon lokaci wajibi ne don baiwa kowa Haƙƙin kamawa da kashewa. An kafa dokar cancantar kama dabbobi daji, ta farko a cikin 1389 ƙarƙashin Richard II. Ya bayyana cewa duk wanda ba shi da filaye ko takardar shela a tsawon shekaru 40, ko malami a kasa da fam 10 a shekara, an hana shi ajiye namun daji ko farauta, da sauran karnukan farauta, da duk wani kayan farauta. Gabatar da dokar ta nuna cewa talakawa sun kasance suna farauta a Ranakun zuwa ibadah lokacin da manyansu suka halarci coci don Bautar kiristoci kuma waɗannan tsarurrukan suna sabbaba tashin hankali a cikin al’umma. An kara yin karin haske game da cancantar mutane a ƙarƙashin James I da kuma Charles II. Waɗannan sabbin dokokin sun haɓaka ƙimar dukiya don kiyaye dabbobin farauta. Har ila yau, ya gabatar da cancantar musamman da suka shafi barewa, zomaye, ciyayi, da ɓangarorin. Dokokin wasa irin su Dokar Farautar Dare ta Burtaniya ta 1828 da Dokar gandun daji 1831, dukansu har yanzu suna kan aiki a cikin tsarin da aka gyara, kuma har yanzu suna da sauran magabata, irin su sanannen Dokar Baƙar fata ta 1723, sun zartar da hukunci mai tsauri don farauta. Amma Dokar dajin da aka sanya a ƙarƙashin William IV ta rage girman dokokin dajin: wajibcin kowane mutum don cancantar kamun namun daji, sai dai daga an soke dokar mallakar takardar shiga daji, kuma an ba wa kowa haƙƙin kashe dabbobin daji a ƙasarsa, ko kuma ta wani da izini.