Dokar Biza ta Burundi | |
---|---|
visa policy (en) | |
Bayanai | |
Ƙasa | Burundi |
Baƙi zuwa Burundi na iya karbar viza a lokacin isar su ko Visa ta yanar gizo sai dai idan sun kasance 'yan ƙasa daga cikin ƙasashe da aka haramtawa visa.
Masu riƙe da fasfo na yau da kullun na ƙasashe masu zuwa na iya shiga Burundi ba tare da biza ba na tsawon watanni 3:
1 - Har ma da, 'yan Kungiyar Tattalin Arziki na Manyan Ruwaye masu rike da laissez-passer.
Masu riƙe da fasfo na diflomasiyya na Turkiyya da fasfo na diflomasiyyar ko na aiki na Brazil, [1] China [2] da Rasha [3] ba sa buƙatar biza. Masu riƙe da fasfo don harkokin jama'a na kasar Sin ba sa buƙatar biza.[2]
An sanya hannu kan yarjejeniyar cire dokar biza ga kasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) a cikin watan Janairun 2019, amma har yanzu dokar ba ta fara aiki ba.
Kasar Burundi ta sanya hannu akan yarjejeniyar cire biza ga masu rike da fasfo na diflomasiyya, aiki da kuma fasfo na yau da kullun ga asar Chadi a ranar 19 ga Yulin 2024, kuma har yanzu dokar ba ta fara aiki ba.
'Yan ƙasa na wasu ƙasashe da yankuna na iya samun biza a lokacin da suka isa ko dai a Filin jirgin sama na Bujumbura (Melchior Ndadaye) ko kuma a sauran iyakokin ƙasar don zama na wucin gadi na tsawon wata 1.[4][5]
'Yan wasu ƙasashe da yankuna na iya samun Bizar Yanar Gizo.[6]
Fasinjoji da ke dauke da tikitin cigaba wanda aka tantance don tafiyar jirgi zuwa ƙasar talakawa. Dole ne su tsaya a yankin sufuri na kasa da kasa na filin jirgin sama kuma ya zamana suna da takardun da ake buƙata ta kasar da zasu sauka.