![]() | |
---|---|
Rayuwa | |
Cikakken suna | Ejike Asiegbu |
Haihuwa | Najeriya, 20 century |
ƙasa | Najeriya |
Harshen uwa | Harshen, Ibo |
Ƴan uwa | |
Abokiyar zama |
Ogechi Asiegbu (en) ![]() |
Yara |
view
|
Karatu | |
Makaranta | jami'ar port harcourt |
Matakin karatu |
Bachelor of Arts (en) ![]() Digiri |
Harsuna |
Turanci Harshen, Ibo Pidgin na Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | jarumi, darakta da ɗan wasan kwaikwayo |
Kyaututtuka | |
Imani | |
Addini | Kiristanci |
IMDb | nm2150200 |
Ejike Asiegbu jarumin fina-finan Najeriya ne kuma daraktan fina-finai wanda ya taba zama shugaban kungiyar 'yan wasan kwaikwayo ta Najeriya.[1][2] A baya an nada shi a matsayin mataimaki na musamman ga tsohon shugaban kasar Biafra Odumegwu Ojukwu a yayin taron tsarin mulkin kasa na 1994 a Abuja.[3]
Ejike Asiegbu ya yi karatun firamare a makarantar constitution Crescent Primary da ke Aba, jihar Abia a Najeriya, amma ya kammala karatun firamare a makarantar St. Mary's Primary School da ke Lokoja a jihar Kogi . Bayan kammala karatun firamare, Ejike Asiegbu ya wuce Kwalejin tunawa da Abdul Azeez Attah da ke Okene a Jihar Kogi a Najeriya, amma ya kammala karatunsa na sakandare a Christ the King College (CKC) da ke Onitsha a Jihar Anambra a Najeriya a shekarar 1980.
Bayan kammala karatunsa na Sakandare, Ejike Asiegbu ya wuce Jami’ar Fatakwal da ke Jihar Ribas a Najeriya inda ya kammala digirinsa na farko a fannin wasan kwaikwayo a shekarar 1993.
Ejike Asiegbu ya shiga masana’antar fina-finan Najeriya (Nollywood) a shekarar 1996 kuma ya yi fim a fim dinsa na farko mai suna “Silent Night” wanda ya fito da shi a fili. Ya fi yawan yin fina-finai tare da Pete Edochie, Clem Ohameze, Kanayo O Kanayo da Kenneth Okonkwo.
Ejike Asiegbu ya lashe kyaututtuka da dama da suka hada da; Mafi kyawun ɗan wasan kwaikwayo na shekara a lambar yabo ta Afirka Magic Viewers Choice Awards,
Ejike yana auren Ogechi Asiegbu, kuma yana da ‘ya’ya hudu, ciki har da Etochi Ejike Asiegbu.