Eldon Maquemba | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Haihuwa | Benguela, 8 ga Yuni, 1984 (40 shekaru) | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
ƙasa | Portugal | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Harshen uwa | Portuguese language | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Karatu | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Harsuna | Portuguese language | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Muƙami ko ƙwarewa | wing half (en) |
Eldon Martins Maquemba, wanda aka sani da Maquemba (an haife shi a ranar 8 ga watan Yuni 1984), ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na ƙasar Angola wanda yake taka leda a matsayin ɗan wasan gaba kuma a matsayin winger. Har ila yau, yana da shaidar zama dan kasar Portugal.
An haifi Maquemba a Benguela, Angola. Ya fara babban aikinsa tare da kulob ɗin Clube Oriental de Lisboa, a cikin rukuni na biyu na Portuguese.[1] kuma ya taka leda a gasar guda daya tare da kungiyoyi Clube Desportivo dos Olivais e Moscavide, AD Portomosense, Imortal Desportivo Clube.
A cikin shekarar 2007, Maquemba ya sanya hannu tare da ƙungiyar Sweden Bodens BK. Bayan shekara guda, ya koma Ingila don buga wasa a kulob ɗin Halesowen Town FC A kakar 2008 – 09, ya sanya hannu a kulob ɗin Olympiakos Nicosia a Cyprus kuma an sayar da shi a cikin watan Janairu 2009 zuwa kulob ɗin Clube Recreativo da Caála a Angola. A cikin watan Janairu 2010, ya kusa sanya hannu kan yarjejeniyar shekaru biyu tare da Peñarol na Uruguay[2] amma ya sanya hannu tare da kulob din Vietnamese Đồng Tâm Long An FC [3] A cikin shekarar 2010, Maquemba ya lashe Kofin BTV tare da Đồng Tâm Long An, bayan nasara akan Matsubara daga Brazil.
A cikin shekarar 2012 Maquemba ya koma Angola, ya sanya hannu kan yarjejeniyar shekaru biyu tare da Progresso Associação do Sambizanga a Girabola.
A cikin shekarar 2016, Maquemba ya koma kulob din Syrianska FC na Sweden. [4]
A watan Nuwamban 2004, Maquemba na cikin tawagar wucin gadi ta Angola mai mutum 29 da za ta buga wasan karshe na cin kofin COSAFA.[5]
Tam Long An
Angola