![]() | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 1970 (54/55 shekaru) |
Karatu | |
Makaranta |
University of Ghana University of Surrey (en) ![]() |
Sana'a | |
Sana'a | Marubuci |
Elizabeth-Irene Baitie (an haife ta a shekarar alif 1970),[1] marubuciya ce na littattafan labaran matasa da 'yammata 'yar kasar Ghana.
Bayan ta halarci makarantar Achimota, Baitie ta karanci ilimin kimiya da ilmin sunadarai a Jami'ar Ghana, Legon, sannan ta sami digiri na biyu a fannin ilimin kimiya na kwaleji daga Jami'ar Surrey kuma yanzu haka tana gudanar da dakin gwaje-gwaje na likita a Adabraka.[2] Tana son rubuta labarai tun tana ɗan shekara bakwai[3] kuma ta dace da rubuce-rubucen ta game da aikinta na yau da kullun da rayuwar iyali a Accra tare da yara uku da miji. Tana rubutu bayan aiki, a karshen mako da kuma lokacin tafiya.[3]
Ta lashe lambar yabo ta First Burt Award don Marubutan Afirka wanda Kungiyar Kanada don Cigaba ta hanyar Ilimi tare da tallafi daga Hukumar Kula da Littattafan Matasa ta Duniya (IBBY):[4] a shekara ta 2009 game da littattafanta na The Twelfth Heart sannan kuma a 2012 game da The Dorm Challenge.[5] The Twelfth Heart ta ci gaba da sayar da kwafi 35,000 a cikin shekaru biyu bayan kyautar. A shekara ta 2006 Baitie ta lashe kyautar Macmillan for Africa (akan Kananan Dalibai) a dalilin littafinta "A Saint in Brown Sandals",[6] kuma shekaru hudu da suka gabata littafin Lea's Christmas ya kasance cikin jerin sunayen 'Marubutan Macmillan na 2002 ga Afirka (Manyan Karatu).[7] An sanar cewa akwai marubuta mata da yawa a Ghana fiye da shekarun da suka gabata, kuma lambobin yabo da aka basu game da aikinsu sun ba da gudummawa kwarai a nasarar su da ƙarfafawa mawallafa wajen siyansu.[8]
Baitie tana rubutu akan yara har ma da matasa. Tana ziyartar makarantu kuma tayi aiki tare da kungiyoyi kamar Gidauniyar Malamai don inganta karatu da littattafai.[9] Tana son ba wa masu karatun ta nishadi da kuma damar tserewa zuwa wata duniya daban, inda ta zabi kar ta jaddada jigon talauci da rashi a cikin littattafan ta, sabanin wasu littattafan matasa a Ghana.[2] A cikin duka The Twelfth Heart da The Dorm Challenge an bayyana taken abokantaka ta hanyar Jin kai ga yarinyar da ta bar ƙaramin ƙauyenta kuma ta sadu da bakin idanu a makarantar da ta shiga.