Elmarie Fredericks (An haife ta a ranar 11 ga watan Agustan shekara ta 1986) ƴar wasan ƙwallon ƙafa ce ta Namibia wacce ke taka leda a matsayin mai gaba ga ƙungiyar mata ta ƙasar Namibia . Ta kasance daga cikin tawagar a Gasar Cin Kofin Mata ta Afirka ta 2014. A matakin kulob din ta buga wa Okahandja Beauties a Namibia.[1][2]