Emil Sambou | |||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||
Haihuwa | 11 Mayu 1994 (30 shekaru) | ||||||||||||||||||||||
ƙasa | Gambiya | ||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||
Muƙami ko ƙwarewa | Ataka |
Emil Sambou (an haife shi ranar 11 ga watan Mayun, 1994) ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne ɗan ƙasar Gambia wanda ke buga wasan gaba a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Afirka ta Kudu Engen Santos FC da kuma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Gambia.
Sambou ya koma Santos bayan nasarar jarrabawar gwaji da ƙwarewar fasaha a lokacin rani na shekarar 2016.[1] Bayan ya shiga kungiyar, dan wasan ya yi hasashen cewa zai zura kwallaye 15 a kakar wasa ta farko a kungiyar. [2]
Ya zura kwallaye biyu a ragar Cape Town All Stars a wasan da suka tashi 3-3. [3]
An kira Sambou zuwa tawagar kwallon kafar Gambia domin buga wasan zagaye da Senegal.[4]
Ya zura kwallaye biyu a wasan sada zumunci da Gambia a wasan da suka doke Gambiya Ports Authority FC 3-2.[5]