Enitan Ransome-Kuti | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Lagos,, 1964 (59/60 shekaru) |
Karatu | |
Makaranta |
Makarantar Sojan Najeriya Jami'ar Tsaron Nijeriya |
Harsuna |
Turanci Yarbanci |
Sana'a | |
Digiri | brigadier general (en) |
Enitan Ransome-Kuti (an haifeshi a shekara ta 1964) hafsan sojan Najeriya ne kuma ɗan marigayi mai fafutukar kare hakkin dan Adam Beko Ransome-Kuti.[1] A cikin shekara ta 2015, ya yi aiki a matsayin kwamandan rundunar haɗin gwiwa ta kasa da kasa.[2]
An haifi Enitan a birnin Legas. Tsohon dalibi ne a Makarantar Soja ta Najeriya da ke Zaria da kuma Makarantar Tsaro ta Najeriya inda ya yi karatun boko kafin ya samu aikin sojan Najeriya, a Najeriya.[3]
Bayan ya tashi daga muƙamin soja zuwa babban birgediya Janar, an naɗa Enitan kwamandan rundunar haɗin gwiwa ta kasa da kasa.[4] A ranar 15 ga watan Oktoba, 2015, wata kotun soji ta sallame shi daga aikin sojan Najeriya tare da yanke masa hukuncin ɗaurin watanni shida a gidan yari bayan samunsa da laifin " tsorata_(tsoro ya hana ya fuskanci abokan gaba) " da " tawaye "[5] bayan harin Baga da kungiyar Boko Haram ta kai a shekarar 2015.[6][7] Sai dai an sassauta hukuncin da aka yanke masa da kuma korar shi a ranar 3 ga watan Maris 2016, kuma an rage mashi matsayi zuwa muƙamin Kanal.[8]