![]() | |||
---|---|---|---|
ga Yuli, 2003 - Mayu 2007 ← ABC Nwosu (en) ![]() | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | 28 Disamba 1944 (80 shekaru) | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Karatu | |||
Makaranta |
University of Rochester (en) ![]() Jami'ar Ibadan Lancaster University (mul) ![]() | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa | ||
Employers | Jami'ar Ibadan |
Eyitayo Lambo an nada shi Ministan Lafiya na Tarayyar Najeriya a watan Yulin shekarar 2003, inda yayi ta rike mukamin har zuwa Mayun shekarar 2007 a lokacin wa’adi na biyu na shugabancin Olusegun Obasanjo.
An haifi Lambo a ranar 28 ga watan Disamban shekarar 1944 a Isanlu, hedkwatar karamar hukumar Yagba ta Gabas a Jihar Kogi, Najeriya. Ya halarci Jami'ar Ibadan, Jami'ar Rochester (Amurka) da Jami'ar Lancaster (UK).
Ya sami digirin farko B.Sc. da na biyu MA duk a fannin tattalin arziki da kuma digirin digir-gir (Ph.D) a fannin bincike na aiki da ya shafi tsarin kiwon lafiya.
Farfesa Lambo ya koyar a matakin farko da na digiri a jami'o'in Ibadan, Ilorin, da Jihar Bendel, a tsakanin shekarun 1974 zuwa 1992.