Faouzia Charfi | |||
---|---|---|---|
1995 - 2001 ← Mohamed Jaoua (en) | |||
Rayuwa | |||
Cikakken suna | Faouzia Farida Rekik | ||
Haihuwa | Sfax (en) , 30 Disamba 1941 (82 shekaru) | ||
ƙasa |
French protectorate of Tunisia (en) Tunisiya | ||
Ƴan uwa | |||
Abokiyar zama | Mohamed Charfi 2008) | ||
Karatu | |||
Makaranta |
Science Faculty of Paris (en) 1963) licence (en) Faculty of Sciences of Tunis (en) doctorate (en) | ||
Harsuna |
Larabci Faransanci | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa, physicist (en) da university teacher (en) | ||
Employers |
Tunis El Manar University (en) École normale supérieure Paris-Saclay (en) | ||
Kyaututtuka |
Faouzia Farida Charfi, (an haife ta a shekara ta 1941 a Sfax, née Rekik) . masaniya ce a fannin kimiyya, 'yar ƙasar Tunisiya, ƙwararriyar ƴa' siyasa. Ta kasance ƙaramar ministar ilimi a shekarar 2011.
Charfi ta kammala karatu daga Sorbonne, Paris, a shekara ta 1963 a fannin kimiyyar jiki, sannan ta sami digiri na uku a shekarun 1978 da 1984 daga Faculty of Science of Tunis wanda wani ɓangare ne na Jami'ar Tunis El Manar.[1] Ta zama ƙaramar ministar ilimi ta Tunisiya a shekara ta 2011.[1][2][3][4]
A cikin shekarar 1997 an naɗa ta Chevalier de la Légion d'Honneur, kuma a cikin shekarar 2001 an naɗa ta Commandeur des Palmes Académiques.[1] A cikin shekarar 2019 an ba ta lambar yabo ta shugabar Cibiyar Duniya ta Larabawa don amincewa da aikinta na yaki da tsattsauran ra'ayin Musulunci.[5][3]
Mijin Charfi shi ne Mohamed Charfi (1936–2008), masanin ilimi kuma ɗan siyasa ɗan ƙasar Tunisiya.[5]