Fatiha Boudiaf (Nuwamba 28, 1944 a Oran) 'yar gwagwarmayar Aljeriya ce, gwauruwa kuma mata ta biyu ga tsohon shugaban ƙasar Aljeriya Mohamed Boudiaf. Bayan kashe shi a shekarar 1992, ta kafa gidauniyar Boudiaf don yaɗa sakon zaman lafiya na mijinta. Ta kasance mai sukar lamirin hukuncin da aka yanke wa Lambarek Boumaarafi, inda ta ce an haɗa baki da yawa wajen kisan tsohon mijin nata kuma ta buƙaci a sake buɗe bincike.
Boudiaf ita ce matar shugaban ƙasar Aljeriya Mohamed Boudiaf ta biyu.[1] Ta yi Allah-wadai da binciken da aka yi a hukumance na kisan maigidanta, wanda ke nuni da cewa ba aikin wani mai son rai ba ne kawai, amma wani ɓangare ne na wani babban shiri. Ta yi yunkurin ziyartar Lambarek Boumaarafi, mutumin da aka samu da laifin kashe mijinta, yayin da yake gidan yari, amma hukuma ta ki amincewa da wannan buƙata.[2]
Ta yi hasashen cewa wanda ya kashe mijinta ya ɓoye a karkashin teburin a gabansa a lokacin kuma har yanzu ba a kama shi ba.[2] A shekarar 2016, ta zargi wasu tsaffin manyan hafsoshin soja huɗu da kisan mijinta, sannan ta aika buɗaɗɗiyar wasika zuwa ga tsohon shugaban ƙasar, Abdelaziz Bouteflika, inda ta buƙaci a sake buɗe shari'ar.[3]
Ta kafa gidauniyar Boudiaf,[4] wacce ta sami lambar yabo ta Yariman Asturias don Hadin gwiwar Duniya a shekarar 1998.[5] An kafa gidauniyar ne domin girmama mijin Boudiaf da ya rasu, kuma yana fatan isar da sakon zaman lafiya da ilimi ga ɗaukacin al'ummar ƙasar Aljeriya. Kowace shekara a ranar zagayowar mutuwarsa, ana bikin rayuwarsa.[6]