Fatumata Djau Baldé | |||||
---|---|---|---|---|---|
2003 - 2003
| |||||
Rayuwa | |||||
ƙasa | Guinea-Bissau | ||||
Karatu | |||||
Harsuna | Portuguese language | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | ɗan siyasa |
Fatumata Djau Baldé ta kasance ministar harkokin wajen Guinea-Bissau har sai da aka yi juyin mulki a watan Satumban 2003.
Ta ɗauki muƙamai da dama a gwamnatin Guinea Bissau. Ta kasance Sakatariyar Haɗin Kan Jama'a da Samar da Aiki, Ministar yawon buɗe ido da kuma Ministar Harkokin ƙasashen Waje. [1] Ta kasance ministar harkokin waje a gwamnatin shugaba Kumba Yala da aka zaɓa, amma mulkinta ya takaita ne saboda an yi juyin mulkin soja a watan Satumban shekarar 2003.[2]