![]() | |||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|
2001 - 2002
| |||||||
Rayuwa | |||||||
Haihuwa | 1 ga Maris, 1969 (55 shekaru) | ||||||
ƙasa | Guinea-Bissau | ||||||
Karatu | |||||||
Harsuna | Portuguese language | ||||||
Sana'a | |||||||
Sana'a | ɗan siyasa |
Filomena Mascarenhas Tipote (an haife ta a ranar 1 ga watan Maris 1969) 'yar siyasar Guinea-Bissauya ce wacce ta yi minista a harkokin waje daga shekarun 2001 zuwa 2002 kuma Ministan tsaro daga shekarun 2003 zuwa 2004.
Firayim Minista Caetano N'Tchama ta naɗa Tipote Sakatariyar Gwamnati a shekarar 2000. Bayan ta yi murabus a ranar 19 ga watan Maris, 2001, an naɗa ta Ministar Haɗin kai, Samar da Aiki da Kula da Talauci ta hannun magajinsa, Faustino Imbali. [1]
Alamara Nhassé ya naɗa Tipote Ministan Harkokin Waje a ranar 9 ga watan Disamba 2001, tana wakiltar Guinea-Bissau a Majalisar Ɗinkin Duniya, [2] kuma tana aiki a cikin wannan aikin har zuwa ranar 17 ga watan Nuwamba 2002. [3] A wannan ranar, an naɗa ta Ministar Gudanarwar Jama'a, Ayyukan Jama'a, Ma'aikata da Aiki a ƙarƙashin Mário Pires, [4] amma Shugaba Kumba Ialá ya kore ta daga wannan aikin a cikin watan Janairu 2003, ba tare da wani dalili ba. [5] Tare da wani canji na gwamnati, Artur Sanhá ya naɗa Tipote Ministar Tsaro a ranar 28 ga watan Satumba 2003, duk da rashin kwarewar soja. [6] Shugabannin sojoji ba su halarci bikin rantsar da ita ba. Ita ce mace ta farko da ta riƙe ofishin kuma ta yi aiki har zuwa ranar 10 ga watan Mayu 2004.[7][8]
Tun daga shekarar 2007, Tipote ta yi aiki tare da shirin Voz di Paz (Voice of Peace), wanda ke mai da hankali kan baiwa Guinea-Bissauan murya a cikin tsarin samar da zaman lafiya. [9]