Folake Olunloyo | |||
---|---|---|---|
| |||
Rayuwa | |||
ƙasa | Najeriya | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa |
Folake Olunloyo-Oshinowo 'yar siyasan Najeriya ce [1] kuma tsohuwar memba a Majalisar Wakilai.[2][3]
Olunloyo-Oshinowo tayi karatu a makarantar St Anne Grammar School da kuma makarantar St International School da ke Ibadan kafin daga bisani ta halarci jami’ar Obafemi Awolowo. Ta kammala karatun a shekarar 1990.[4]Ta kasance babbar mataimakiya ga tsohon kakakin majalisar, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal, kafin ta sauya sheka daga jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zuwa All Progressive Congress (APC).[5]
Olunloyo-Oshinowo riqe da jigon lakabi na Aare Egbe Omo Iyalode. ta auri Dakta Tunde Oshinowo.[6]
A shekarar 2011 aka zabe ta ta zama yar majalisar wakilai. Sauran da suka samu nasarar zama 'yan majilar sun hada da Suleiman Oba Nimota, Maimunat Adaji, Martha Bodunrin, Betty Okogua-Apiafi, Rose Oko da Nkoyo Toyo.[7]