Blueprint gidan jarida ne a Najeriya, wanda suke yaɗa labaran su a kullum. Babban hedkwatar gidan jaridar yana Abuja. Gidan Jaridar ta fara ne da watsa labarai mako-mako a watan Mayun shekarar 2011, sannan ta koma watsa labaranta kullum-kullum a cikin watan Satumba duk dai a cikin shekarar 2011. Jaridar tana yaɗa labarai kashi biyu, yaɗawa na farko shine wanda zasu cire jaridar dake ɗauke da labarai na kullum-kullum na takarda. Sai kuma bugawa ta biyu itace wadda suke yaɗa labarai a kafar sada zumunta ta yanar gizo kamar irin su fesbuk, tuwita da sauran su, suna sabunta labaran su na kafar sada zumunta zamani a duk lokacin da wani labari ya samu.[1][2][3][4][5]