Gidan Kayan Tarihi Na Birnin Benin | |
---|---|
Wuri | |
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya |
Jiha | Edo |
Birni | Kazaure |
Coordinates | 6°19′59″N 5°37′20″E / 6.332922°N 5.622252°E |
History and use | |
Opening | 1973 |
Manager (en) | Hukumar Kula da Gidajen Tarihi ta Kasa |
Contact | |
Address | Kings Square, Ring Rd, Avbiama 300102, Benin City |
|
Gidan tarihi na birnin Benin babban gidan kayan tarihi ne na kasa a cikin birnin Benin, Najeriya.[1] dake tsakiyar birnin kan dandalin Sarki.[2] Gidan kayan tarihin yana da adadi mai yawa na kayan tarihi masu alaƙa da daular Benin kamar terracotta, sifofin tagulla da simintin ƙarfe. Har ila yau, yana da tsohuwar fasaha da ke da alaƙa da zamanin farko.[3]
Gidan tarihi na birnin Benin yana wani wuri da ake kira Ring Road wanda a da mutanen Benin ke kiransa da dandalin Sarki, to amma Kwamared Adams Oshiomhole ya canza shi zuwa dandalin Oba Ovonramwen a lokacin yana gwamnan jihar.[4] [5]