Ginigeme Francis Mbanefoh | |
---|---|
Rayuwa | |
Harshen uwa | Harshen, Ibo |
Mutuwa | 8 ga Faburairu, 2017 |
Karatu | |
Harsuna |
Turanci Harshen, Ibo |
Sana'a |
Ginigeme Francis Mbanefoh malami ne a Najeriya. Ya yi aiki a matsayin shugaban Jami'ar Najeriya Nsukka na 11.[1] Ya fito ne daga Eziowelle, Idemili na jihar Anambra. Ya gaji Umaru Gomwalk. Ya shigo ne a daidai lokacin da aka ce jami’ar ta shiga cikin mawuyacin hali.[2] An yaba masa saboda kusancinsa da jama’arsa da kuma yadda ya baiwa al’ummar wannan cibiya damar sanin ya kamata, lamarin da ya ba shi lakabin gargajiya daga garinsa da kuma Majalisar Sarakunan Gargajiya ta shiyyar Nsukka[3]. Kundin karatunsa na PhD mai suna Allocation of Road Funds in Nigeria: An Evaluation, wanda aka bayar a shekarar 1976.[4] Ya rasu ne a ranar 8 ga Fabrairu, 2017. An yi jana’izar sa a kasarsa ta Eziowelle a ranar 5 ga Mayu, 2017, ya samu halartar manyan baki daga sassan tarayyar kasar nan.