Gladys Anoma | |||
---|---|---|---|
| |||
Rayuwa | |||
Cikakken suna | Gladys Rose Bonful | ||
Haihuwa | Grand-Bassam (en) , 28 ga Maris, 1930 | ||
ƙasa | Ivory Coast | ||
Mutuwa | 15th arrondissement of Paris (en) , 26 Oktoba 2006 | ||
Karatu | |||
Makaranta | University of Paris (en) | ||
Harsuna | Faransanci | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa |
Gladys Anoma (1930 - Oktoba 26, 2006) farfesa ce mai ilimin kimiyya kuma 'yar siyasa ce daga Ivory Coast a Yammacin Afirka.[1]
Anoma 'yar Joseph Anoma ce, kuma yayin da daga baya aka san ta da Gladys Anoma, an ba ta suna Bonful Gladys Rose Anoma lokacin haihuwar ta.[1] Ta kasance ɗaliba a Senegal na tsawon shekaru huɗu sannan a Faransa na tsawon shekaru biyu.[1] Ta sami digiri na uku a fannin tsirrai na wurare masu zafi[2] daga Sorbonne, a Paris, Faransa, sannan ta ziyarci Tunisiya, Jamus, Ingila, Habasha, Morocco da Ghana kafin ta kai shekaru 37.[3]
A cewar labarin ta, ta yi aure da HE Ambassador J. Georges Anoma. Kuma taana da ’yar’uwa mai suna Mrs. Aké.[3]
Rahoton wata jarida game da balaguron mako biyar da ta yi zuwa Kingston, New York a watan Agusta 1968, tare da wasu shugabannin mata 11 na Afirka, ta ce mijinta, a lokacin, shi ne Sakatare Janar na Ma’aikatar Harkokin Waje kuma ma’auratan suna 'ya 'ya huɗu. Makasudin tafiyar shi ne don gano "al'amurra masu tada hankali a Amurka da Afirka."[3]
Ta rasu a birnin Paris a shekara ta 2006 kuma an binne ta a Abidjan na ƙasar Ivory Coast.[4] An gudanar da bikin tunawa da ita a cocin Saint Jacques Two Plateaux for Anoma a cikin shekarar 2016, shekaru 10 bayan mutuwarta.[3]