Gold Coast Lounge (fim) | |
---|---|
![]() | |
Asali | |
Lokacin bugawa | 2020 |
Asalin suna | Gold Coast Lounge |
Asalin harshe | Turanci |
Ƙasar asali | Ghana |
Characteristics | |
Genre (en) ![]() |
neo-noir (en) ![]() |
Direction and screenplay | |
Darekta | Pascal Aka |
Marubin wasannin kwaykwayo | Pascal Aka |
'yan wasa | |
External links | |
Specialized websites
|
Gold Coast Lounge fim din neo-noir ne na Ghana na shekarar 2020 wanda Pascal Aka ya rubuta kuma ya ba da Umarni, haka-zalika ya fito a cikin fim ɗin. Sauran fitattun jaruman shirin sun haɗa da, Alphonse Menyo, Adjetey Anang, Zynnell Zuh, Raquel.[1][2][3]
Gidan shakatawa na Gold Coast, wanda ƙungiyar masu aikata laifuka ta John Donkor ke gudanarwa, sanannen wuri ne ga masu aikata laifuka na Ghana ƴan mulkin mallaka. Da samun ƴancin kai na kasar, sabuwar gwamnati ta yi barazanar rufe falon. A wannan lokacin, Donkor da kansa yana gidan yari, tare da ɗakin kwana a ƙarƙashin jagorancin Laftanar Donkor, Daniel da Wisdom.
Dukansu waɗanda Donkor suka shigar da su tun suna ƙanana, Daniel da Wisdom, ba da daɗewa ba suka fara fafatawa mai zafi da ta ci gaba har wa yau. Hasalima ta ƙara tsananta yayin da Donkor ya ɗauki Daniel a matsayin magajinsa, wanda ya ƙara nisantar daga Wisdom.
Bayan an kashe shugabansu, dole ne babba ya karbi mulki, sannan a zo a yi tawaye da bincike.[4][5][6][2]
A shekara ta 2019, fim ɗin ya lashe kyautuka takwas a cikin Kyautar Fina-Finan Ghana sannan kuma ya lashe kyaututtuka shida a Kyautar Fina-Finan Golden a 2020.2020.[7]