Kyautar fina-finai na Golden Movies lambar yabo ce da ake bayarwa ta shekara-shekara wacce ke nuna bajintar nasarori a talabijin da fina-finai na Afirka.[1] An gudanar da kashi na farko ne a ranar 27 ga watan Yuni 2015 a ɗakin taro na Banquet Hall, Ghana. A watan Mayun 2016, an bayyana Nadia Buari a matsayin jakadiyar lambar yabo.[2] Uti Nwachukwu da Selly Galley ne suka ɗauki nauyin taron na 2016 a ranar 25 ga watan Yuni.[3]