Guessouma Fofana | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Haihuwa | Le Havre, 17 Disamba 1992 (31 shekaru) | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
ƙasa |
Faransa Mali Muritaniya | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Ƴan uwa | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Ahali | Gueïda Fofana (en) | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Karatu | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Harsuna | Faransanci | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Muƙami ko ƙwarewa | Mai buga tsakiya | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Lamban wasa | 76 | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Nauyi | 77 kg |
Guessouma Fofana (an haife shi a ranar 17 ga watan Disamban, shekara ta 1992) a Faransa, ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne wanda ke taka leda a matsayin ɗan wasan tsakiya. yana wakiltar Mauritaniya a matakin kasa da kasa.
A watan Agustan shekarar 2018, Fofana ya tafi kulob ɗin En Avant de Guingamp a kwantiragin shekaru uku. An kiyasta kudin canja wurin da aka biya wa Amiens a kan Yuro miliyan 1.[1] A karshen lokacin rani 2019 na transfer window, ya koma kulob ɗin Le Mans a matsayin aro, New promoted Ligue 2.[2]
An kira Fofana ne a tawagar kasar Mauritaniya a watan Nuwamba shekara ta 2021 a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya ta FIFA 2022 da Zambiya da Equatorial Guinea.[3] Ya fara wasa da Mauritania a wasan da a ka tashi 1-1 da Equatorial Guinea a ranar 16 ga watan Nuwamban 2021.[4]
tawagar kasar Mauritania | ||
---|---|---|
Shekara | Aikace-aikace | Manufa |
2021 | 4 | 0 |
2022 | 4 | 0 |
Jimlar | 8 | 0 |
An haife shi a Faransa, Fofana dan asalin Mauritaniya ne da kuma Mali.[5] Shi da ɗan'uwansa 'yan wasan ƙwallon ƙafa ne Gueida da Mamadou Fofana.[6]
Guingamp
Cluj CFR