Gwagwalada | ||||
---|---|---|---|---|
| ||||
Wuri | ||||
| ||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | |||
Jihohin Najeriya | Babban Birnin Tarayyan Najeriya, | |||
Labarin ƙasa | ||||
Yawan fili | 1,043 km² | |||
Bayanan Tuntuɓa | ||||
Lambar aika saƙo | 902101 | |||
Kasancewa a yanki na lokaci | ||||
Wasu abun | ||||
| ||||
Yanar gizo | fctacss.org.ng… |
Gwagwalada karamar hukumace a babban birnin tarayyar Najeriya Abuja, tana daya daga cikin kananan hukumomi biyar da suke a babban birnin tarayya.[1]
Gwagwalada tana da fadin kasa kilomita 1,043 2 kuma tana da yawan jama'a 158,618 a kidayar shekarar 2006. Ana hasashen za ta samu ci gaba da kashi 6.26 cikin 100 tsakanin shekarar 2020 zuwa 2025, wanda shine karuwar mafi girma a nahiyar Afirka. Kafin a kafa babban birnin tarayya Gwagwalada tana karkashin gundumar Kwali ta tsohuwar masarautar Abuja wacce a yanzu take a Suleja.[2] An kirkiro Gwagwalada ne a ranar 15 ga Oktoba 1984. Adadin jama'arta a hukumance ya kai mutane 158,618 a kidayar 2006.[3]