Hafez Makhlouf | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Damascus, 2 ga Afirilu, 1971 (53 shekaru) |
ƙasa | Siriya |
Ƴan uwa | |
Mahaifi | Mohammed Makhlouf |
Ahali | Rami Makhlouf (en) , Iyad Makhlouf (en) da Ihab Makhlouf (en) |
Karatu | |
Harsuna | Larabci |
Sana'a | |
Sana'a | soja da ɗan siyasa |
Aikin soja | |
Fannin soja | Syrian Arab Army (en) |
Digiri | colonel (en) |
Imani | |
Jam'iyar siyasa | Arab Socialist Ba'ath Party – Syria Region (en) |
Hafez Mohamad Makhlouf ( Larabci: حافظ مخلوف An haife shi a ranar 2 ga watan Afrilun Shekarar 1971), wanda kuma aka fi sani da Hafez Makhlouf, wani Kanar ɗan kasar Siriya ne mai ritaya kuma tsohon jami'in leƙen asiri wanda ya kasance shugaban reshen Damascus na Babban Daraktan Leken Asiri na kasar Siriya .[1][2]Ya kasance memba na shugaban Sitiya Bashar al-Assad "na kusa" magoya bayansa.[3]
An haifi Makhlouf a Damascus a ranar 2 ga watan Afrilun shekarar 1971. [4] Shi ɗan uwa ne ga shugaban ƙasar Siriya, Bashar al-Assad kuma ɗan uwan Rami Makhlouf, babban ɗan kasuwan Siriya. Haka kuma ɗan uwa ne ga Atef Najib, babban jami'in tsaron siyasa a birnin Daraa . [5] An ba shi aiki a cikin Rundunar Tsaro ta Republican a cikin shekarar 1992 kuma abokin Bassel al-Assad ne. Makhlouf ya ji rauni ne a wani hatsarin mota mai tsauri a shekarar 1994 wanda ya yi sanadiyyar mutuwar babban wan Bashar al-Assad, Bassel al-Assad.[6]
Makhlouf ya kasance Kanar na Sojoji kuma shugaban hukumar leƙen asiri a reshen Babban Daraktan Tsaro na Damascus har zuwa shekarar 2014.[7][8]
Ma'aikatar Baitulmali ta kasar Amurka ta sanya wa Makhlouf takunkumi a shekara ta 2007 saboda "raguza diyaucin Lebanon ko tsarin dimokuraɗiyya da cibiyoyi." Takunkumin ya yi kira da a daskare “duk wata kadarorin da waɗanda aka zayyana suka samu a kasar Amurka”, kuma sun haramta wa mutanen Amurka yin mu’amala da waɗannan mutane.”[9]A cikin shekarar 2011 kasar Amurka ta ƙara sanyawa Makhlouf takunkumi a watan Mayu, EU a watan Satumba. [1] A watan Nuwambar shekarar 2011 ne ƙungiyar ƙasashen Larabawa ta sanya masa takunkumin tafiye-tafiye. [1]
Hukumomin Switzerland sun daskarar da asusun Hafez Makhlouf na kimanin Euro miliyan 3 a wani bankin Geneva bisa zargin karkatar da kuɗaɗe a shekarar 2011. [10] A cikin watan Fabrairun 2012, Makhlouf ya yi nasara a wata doka ta neman warware SFr miliyan 3 (dala miliyan 3.3) da ke cikin asusun banki a kasar Switzerland bayan ya daukaka kara, yana mai cewa hakan ya riga ya sanya takunkumi. [10] Sai dai kuma kotun kolin Switzerland ta ki amincewa da bukatarsa ta doka ta shiga Switzerland don ganawa da lauyoyinsa a ƙarshen shekara ta 2011.[11]
An bayar da rahoton cewa, Hafez Makhlouf ya sayi fam miliyan 31 a cikin kadarori na kasar Moscow ta hanyar hada-hadar kuɗi na ɗan kasuwan Syria-Rasha Mudalal Khoury .
A ranar 18 ga watan Yulin shekarar 2012, Al Arabiya ta bayar da rahoton cewa, an kashe Makhlouf a wani harin bam da aka kai kan wani taro na Cibiyar Kula da Rikice-Rikice (CCMC) a hedkwatar tsaron ƙasar Syria da ke Damascus. [12] Sai dai wasu majiyoyi sun nuna cewa ya samu rauni ne kawai a harin.[13]
A cikin watan Satumbar shekarar 2014, majiyoyi masu yawa sun ruwaito cewa ya koma Belarus tare da matarsa. A farkon watan, an cire Makhlouf daga muƙaminsa na leƙen asiri mai ƙarfi a Damascus amma majiyoyi masu goyon bayan gwamnati sun ce wani mataki ne na yau da kullum. Joshua Landis, wani masani ɗan ƙasar Amurka kan Syria ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa Makhlouf ya bar ƙasar Syria kuma shi da ɗan uwansa Ihab sun cire hoton Assad daga shafukansu na Facebook da kuma bayanan WhatsApp.[14][15]