Hafsa Hatun | |||
---|---|---|---|
| |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Selçuk (en) , 1380 | ||
ƙasa | Daular Usmaniyya | ||
Mutuwa | Bursa, 1403 | ||
Ƴan uwa | |||
Mahaifi | İsa Bey | ||
Abokiyar zama | Bayezid I (en) | ||
Sana'a | |||
Sana'a | aristocrat (en) |
Ka duba wannan shafin domin sanin yanda zaka gyara wannan mukalar Koyon rubuta mukala
Akwai yuwar admin ya goge wannan shafin matukar ba'a inganta ta ba. |
Hafsa Hatun ( Ottoman Turkish, " matashin zaki ") ƴar ƙasar Turkiyya ce, kuma yar'uwar Bayezid I, Sultan na Daular Usmaniyya .
Hafsa Hatun ɗiyar Isa Bey ce, sarkin Aydinid . Ta yi aure da Bayezid a shekara ta 1390, bayan ya ci Aydinid. [1][2] Mahaifinta ya miƙa wuya ba tare da faɗa ba, aka ɗaura aure tsakaninta da Bayezid. Bayan haka, an kuma aika Isa zuwa gudun hijira a Iznik, wanda ikonsa ya ƙare, inda daga baya ya mutu.[3][4] Aurenta ya ƙara danƙon zumunci a tsakanin iyalai biyu.[5]
Ayyukan jama'a na Hafsa Hatun suna cikin yankin mahaifinta kuma wataƙila an gina su ne kafin ta auri Bayezid. [1] Ta ba da aikin maɓuɓɓugar ruwa a cikin garin Taya da kuma Hermitage a Bademiye, da wani masallaci da aka fi sani da "Hafsa Hatun Mosque" [6] tsakanin shekarata 1390 zuwa 1392 daga kuɗin da ta samu a cikin sadakinta.[7]