Halima Tayo Alao | |||||
---|---|---|---|---|---|
26 ga Yuli, 2007 - 29 Oktoba 2008 ← Helen Esuene - John Odey →
2005 - ga Yuli, 2006 | |||||
Rayuwa | |||||
Haihuwa | 6 Disamba 1956 (67 shekaru) | ||||
ƙasa | Najeriya | ||||
Karatu | |||||
Makaranta |
Jami'ar Ahmadu Bello Jami'ar Ilorin | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | Masanin gine-gine da zane da ɗan siyasa |
Halima Tayo Alao (an haife ta ne a ranar 6 ga watan Disamban shekarar 1956) tsohuwar mai tsara gine-gine ce 'yar Najeriya, kuma tsohuwar Ministar Muhalli da Gidaje a lokacin gwamnatin Shugaba n kasan Najeriya Umaru ' Yar'Adua .
An haifi Halima Tayo Alao a ranar 6 ga Disamban shekarar 1956. Ta samu digiri na biyu a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya a 1981 a fannin gine-gine. Ta shiga aikin farar hula na jihar Kwara a shekarata 1982. Ta zama Babban Sakatariya a Ma’aikatar Ayyuka da Sufuri, Ilorin, Jihar Kwara.[1] Ta samu digiri na biyu a fannin mulki, 2003 daga Jami'ar Ilorin . Daga shekarar 2005 zuwa Yulin 2006, ta kasance Karamar Ministar Lafiya ta Tarayya.[2]
Alao ya shiga aikin farar hula na jihar Kwara a shekaran ta 1982.[3] Ta zama Babban Sakatare a ma’aikatun Kasa da Gidaje na jihar Kwara, sannan Ayyuka da Sufuri. Kafin wannan lokacin, ita kadai ce Shugaba / Shugaban Karamar Hukumar Ilorin ta Kudu kuma Sakatariyar zartarwa, Hukumar Kula da Mata ta Jihar Kwara. Daga watan Yunin a shekara ta 2005 zuwa wayan Yunin shekara ta 2006, ta kasance Karamar Ministar Ilmi ta Tarayya sannan daga baya, ta zama Karamar Ministar Lafiya ta Tarayya.[4][5]
An nada ta a cikin kwamitin UACN Property Debelopment Company Plc a ranar 13 ga watan Janairu, shekara ta 2010 a matsayin darekta ba zartarwa ba. Ta sauka daga shugabancin hukumar ne a shekara ta 2019 [6]
Alao ya nada Ministan Muhalli da Gidaje a ranar 26 ga watan Yulin shekara ta 2007 da Shugaba Umaru 'Yar'Adua. [7] amma an kore shi a cikin babban garambawul a majalisar zartarwa a ranar 29 ga watan Oktoba, shekara ta 2008. [8] An ce korar ta biyo bayan ce-ce-ku-cen da ta ke yi da Chuka Odom, karamin minista kuma wakiliyar jam'iyyar Progressive Peoples Alliance . [9] Wanda ya maye gurbinta shi ne John Odey, wanda aka nada a ranar 17 ga watan Disamba shekara ta 2008. [10]