Hamdi Meddeb

Hamdi Meddeb
Rayuwa
Haihuwa Tunis, 8 ga Afirilu, 1952 (72 shekaru)
ƙasa French protectorate of Tunisia (en) Fassara
Tunisiya
Sana'a
Sana'a ɗan kasuwa da ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
 

Hamdi Meddeb (an haife shi: Mohamed Meddeb a shekarar ta alif dubu daya da dari tara da hamsin da biyu 1952) ɗan kasuwa ɗan Tunisiya ne, mai saka hannun jari, kuma shugaban Esperance Sportive de Tunis na yanzu, ƙungiyar wasanni mafi tsufa a Tunisiya.[1]

Meddeb ya buga wasan ƙwallon ƙafa ga ƙungiyar matasa ta Espérance Sportive de Tunis daga shekarun ta alif dubu daya da dari tara da sittin da bakwai 1967 zuwa shekara 1971.[2]

Hamdi Meddeb

A shekara ta 1978, ya karɓi kasuwancin danginsa kuma ya kafa Kamfanin Tunisiya da Masana'antar Kiwo (Faransa: la Société tunisienne des industries alimentaires, STIAL). A shekara ta 1997, Délice ya haɗu da Danone ya ba shi kashi 50 cikin 100 na hannun jari a cikin kasuwancin don samar da Délice Danone. Ya sayi kashi 30% na kamfanin Vitalait Meddeb tare da hadin gwiwar kamfanin Biritaniya na Virgin Cola a shekarar 2002 don samar da kayan shaye-shaye ga kasuwannin Tunisiya, amma haɗin gwiwar ya ɗauki shekaru huɗu kacal.[3] A shekarar 2014, Meddeb ya gabatar da Délice Holding a cikin Tunis Stock Exchange.[3]


Esperance Sportive de Tunis (EST)

[gyara sashe | gyara masomin]

Bayan shekarun 1990 na Esperance golden age tare da shugaban Slim Chiboub, magoya bayansa sun damu da wanda zai jagoranci kungiyar lokacin da Chiboub ya bar kungiyar a shekarar 2004.[4] Dan kasuwa Aziz Zouhir ya rike shugabancin na tsawon shekaru biyu da watanni tara, daga watan Nuwamba 2004 zuwa watan Agusta 2007.[5] Hamdi Meddeb ya zama shugaban Espérance Sportive de Tunis a ranar 10 ga Agusta 2007.[6] Kafin ya zama shugaban kasa na gaba, Meddeb ya kasance ba a sani ba ga yawancin 'yan Tunisiya, har ma da yawancin magoya bayan EST. Bayan ya yi ritaya daga ƙungiyar matasa ta Esperance a matsayin ɗan wasa a farkon 1970s, Hamdi Meddeb ya sadaukar da kansa ga kasuwancinsa, amma ya kasance kusa da Esperance kuma ya gudanar da ayyuka daban-daban na gudanarwa—ciki har da kasancewa mai ci gaba da ba da kuɗi na ƙungiyar—tsawon shekaru.

A watan Yuni 2021, Meddeb ya bayyana aniyarsa ta yin murabus da barin kungiyar. Yarjejeniya tsakanin membobin da magoya bayansa sun yi watsi da tafiyar tasa. Daga karshe ya sake duba yiwuwar murabus dinsa ya zauna. [7]

Ko da yake Hamdi Meddeb yana yawan gayyata da ganawa da shugabanni da firaministan kasar Tunisia, amma ba kasafai yake fitowa a kafafen yada labarai ba ko kuma ya yi hira da shi.[8] [9]

Bayan rugujewar gwamnatin Tunisia a ranar 14 ga watan Janairun 2011, an zargi wasu 'yan kasuwa da shugabannin masana'antu da cin hanci da rashawa da kuma goyon bayansu ga Zine El Abidine Ben Ali a yakin neman zabensa na shekarar 2009.[10] Abotakar Meddeb da Mohamed Sakher El Materi, surukin Ben Ali, ya sa jita-jita da yawa suka yada game da sunansa na dan kasuwa. Ya yi haɗin gwiwa tare da Matri kuma yana cikin farkon masu saka hannun jari na bankin Zitouna. A cikin watan Nuwamba 2010, Meddeb da Matri sun sayi hannun jari na kashi 25 a Tunisiana (daga baya aka sake masa suna Ooredoo Tunisia).

  1. "Meddeb HAMDI sa biographie" [Meddeb HAMDI his biography.] (in French). ilBoursa. Retrieved 16 September 2021.
  2. Mohammad Imad (2 May 2021). " ﺍﻟﺮﺋﻴﺲ ﺍﻟﺼﺎﻣﺖ .. 5 ﻣﻌﻠﻮﻣﺎﺕ ﻋﻦ ﺣﻤﺪﻱ ﺍﻟﻤﺪﺏ ﺻﺎﻧﻊ ﻧﺠﺎﺣﺎﺕ ﺍﻟﺘﺮﺟﻲ " [The silent president..5 facts about Hamdi Meddeb the engine of the success of L'Espérance Sportive de Tunis] (in Arabic). Al-Ain Newspaper. Retrieved 16 September 2021.
  3. 3.0 3.1 Frida Dahmani (24 September 2014). "Agroalimentaire : Hamdi Meddeb, du football à la Bourse" [The food industry: Hamdi Meddeb, from soccer to the stock exchange] (in Faransanci). Jeune Afrique. Retrieved 16 September 2021.
  4. "Aziz Zouhir nouveau président de l'EST – Tunisie-Foot" . Tunisie-foot.com. Retrieved 2021-12-05.
  5. "Aziz Zouhir nouveau président de l'Espérance"
  6. "Assemblée Générale de EST: Meddeb 15è président de l'EST (Vidéo)"
  7. "Hamdi Meddeb va-t-il quitter l'Espérance Sportive de Tunis?" [Will Hamdi Meddeb quit L'Espérance Sportive de Tunis]. Réalités Online (in French). 2021-06-30. Retrieved 2021-08-24.
  8. ﻟﻘﺎﺀ ﺭﺋﻴﺲ ﺍﻟﺠﻤﻬﻮﺭﻳﺔ ﻣﻊ ﺣﻤﺪﻱ ﺍﻟﻤﺪﺏ ﺭﺋﻴﺲ ﺍﻟﺘﺮﺟﻲ ﺍﻟﺮﻳﺎﺿﻲ ﺍﻟﺘﻮﻧﺴﻲ | ﺭﺋﺎﺳﺔ ﺍﻟﺠﻤﻬﻮﺭﻳﺔ ﺍﻟﺘﻮﻧﺴﻴﺔ " (in Arabic). Carthage.tn. Retrieved 2021-12-05.
  9. Youssef Chahed reçoit Hamdi Meddeb Business News
  10. ﻣﻦ ﻫﻢ ﺍﻟﻤﺴﺆﻭﻟﻮﻥ ﻭﻧﺠﻮﻡ ﺍﻟﺮﻳﺎﺿﺔ ﺍﻟﻤﻮﺭﻃﻮﻥ ﻓﻲ ﻗﻀﺎﻳﺎ ﺑﻌﺪ ﺍﻟﺜﻮﺭﺓ؟ " .