Hamza bin Laden | |
---|---|
Rayuwa | |
Cikakken suna | حمزة بن أسامة بن محمد بن عوض بن لادن |
Haihuwa | Jeddah, 9 ga Yuni, 1989 |
ƙasa |
Saudi Arebiya statelessness (en) |
Harshen uwa | Larabci |
Mutuwa | Ghazni Province (en) , 25 ga Yuli, 2019 |
Yanayin mutuwa | (killed in action (en) ) |
Ƴan uwa | |
Mahaifi | Osama bin Laden |
Mahaifiya | Khairiah Sabar |
Ahali | Saad bin Laden (en) , Omar bin Laden (en) da Khalid bin Laden (en) |
Yare | Bin-Laden Family (en) |
Karatu | |
Harsuna | Larabci |
Sana'a | |
Sana'a | Jihadi |
Mamba | Al-Qaeda |
Aikin soja | |
Ya faɗaci |
War on Terror (en) War in Afghanistan (en) insurgency in Khyber Pakhtunkhwa (en) |
An haifi Hamza bin Laden a shekarar 1989 a Jedda, a cikin kasar Saudi Arabia . A watan Janairun shekara ta alif dubu biyu da daya 2001, Hamza, mahaifinsa da sauran danginsa sun halarci bikin auren ɗan'uwansa Mohammed bin Laden a kudancin birnin Kandahar na Afghanistan . [1] Hoton bidiyo da aka harbe a Lardin Ghazni a watan Nuwamba na wannan shekarar ya nuna Hamza bin Laden da wasu 'yan uwansa suna kula da fashewar jirgi mai saukar ungulu na kasar Amurka kuma suna aiki tare da Taliban.[2]
A watan Maris na shekara ta alif dubu biyu da ukku 2003, an yi iƙirarin cewa Hamza bin Laden da ɗan'uwansa Saad bin Laden sun ji rauni kuma an kama su a Ribat, Afghanistan. Wannan da'awar ta zama ƙarya. Koyaya, Hamza bin Laden da sauran shugabannin Al Qaeda sun nemi mafaka a kasar Iran bayan hare-haren 9/11.