Hawa Abdallah Mohammed Salih | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Sudan, 1984 (40/41 shekaru) |
ƙasa | Sudan |
Sana'a | |
Sana'a | Mai kare ƴancin ɗan'adam |
Kyaututtuka |
gani
|
Hawa Abdallah Mohammed Salih (Larabci : حواء عبد الله محمد صالح) 'yar gwagwarmaya ce 'yar ƙasar Sudan. [1] An haife ta a Arewacin Darfur amma sai da ta fice saboda faɗan da ake yi tsakanin dakarun gwamnati da 'yan tawayen Darfur. [2] Ta koma sansanin 'yan gudun hijira na Abu Shouk, inda ta yi aiki tare da jami'an Majalisar Ɗinkin Duniya da kuma wata kungiya mai zaman kanta ta Amurka IRC don yaɗa bayanai da wayar da kan jama'a game da yanayin sansanin. [2] Domin aikinta an kama ta har sau uku, kuma jami'an tsaron ƙasar sun yi garkuwa da ita sau biyu aka tsare ta, ciki har da wani lokaci a shekarar 2011 da aka tsare ta tsawon watanni biyu tare da azabtar da ita da kuma yi mata fyaɗe a wani gidan yari na ƙasar a birnin Khartoum. [2] [3] Sai da ta gudu daga Sudan a shekarar 2011. [1]
Ta sami lambar yabo ta shekarar 2012 International Women of Courage award. [1] [4]
Ta samu mafaka a Amurka. [5] Mary Gay Scanlon ce ta wakilce ta bisa kyakkyawan tsari, daga baya memba a Majalisar Wakilan Amurka daga Pennsylvania.
<ref>
tag; name "state.gov" defined multiple times with different content