![]() | |
---|---|
![]() | |
Rayuwa | |
Haihuwa |
Ambam (en) ![]() |
ƙasa | Kameru |
Karatu | |
Makaranta |
University of Havana (en) ![]() |
Harsuna |
Faransanci Turanci |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan jarida |
Kyaututtuka |
gani
|
Henriette Ekwe Ebongo (25 ga watan Disambar shekarar 1949) [1] 'yar jarida ce 'yar kasar Kamaru, mawallafiya kuma 'yar gwagwarmayar siyasa. An ba ta lambar yabo ta Mata masu ƙarfin zuciya a cikin shekarar 2011. [2] [3]
Ebongo tana ba da shawarar 'yancin 'yan jarida, daidaiton jinsi, 'yancin ɗan adam, da shugabanci nagari. Ta kasance mai fafutuka a gwagwarmayar yaki da mulkin kama-karya a shekarun 1980, da yakin da ake yi a halin yanzu na yaki da cin hanci da rashawa na gwamnati, wariyar jinsi da take hakkin dan Adam. A wannan lokacin ta sha fama da danniya da azabtarwa da kuma kai ta kotun soji. [2] [4]
Ita ce mawallafiyar jaridar Babela mai zaman kanta ta mako-mako kuma ta kafa kungiyar Transparency International reshen Kamaru, kungiyar da ba ta gwamnati ba.[5]