Hugo Lucien Mamba-Schlick (an haife shi a ranar 1 ga watan Fabrairun shekarar 1982) ɗan wasan triple jumper ne ɗan ƙasar Kamaru mai ritaya.[1]
Ya zo na shida a Gasar Cin Kofin nahiyar Afirka na shekarar 2006, ya lashe lambar azurfa a Gasar Cin Kofin Afirka ta shekarar 2007, ya kuma lashe lambar azurfa a Gasar Cin Kofin yankin Afirka na shekarar 2008.[2] Ya kuma taka leda a gasar cin kofin duniya ta shekarun 2007, 2009 da 2011 ba tare da ya kai wasan karshe ba. A cikin shekarar 2010 ya lashe lambar azurfa a gasar Commonwealth a Delhi, a cikin wani sabon tsalle mai tsayi na mita 17.14. Wannan shine tarihin kasar Kamaru na yanzu.[3]
↑Evans, Hilary; Gjerde, Arild; Heijmans, Jeroen;
Mallon, Bill ; et al. "Hugo Mamba-Schlick Olympic
Results" . Olympics at Sports-Reference.com . Sports
Reference LLC. Archived from the original on 18
April 2020. Retrieved 7 July 2017.