Hussein El Shahat | |||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||
Haihuwa | Kairo, 21 ga Yuni, 1992 (32 shekaru) | ||||||||||||||||||||||
ƙasa | Misra | ||||||||||||||||||||||
Harshen uwa | Egyptian Arabic (en) | ||||||||||||||||||||||
Karatu | |||||||||||||||||||||||
Harsuna |
Larabci Egyptian Arabic (en) | ||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||
Muƙami ko ƙwarewa | Mai buga tsakiya | ||||||||||||||||||||||
Nauyi | 68 kg |
Hussein Ali Elshahat Ali Hassan ɗan kwallon Masar ne wanda ke buga wa ƙungiyar Al Ahly wasa a matsayin dan wasan gefe, yana iya buga wasan tsakiya na gaba.[1]
Elshahat ya bugawa Misr Lel-Makkasa daga 2014 zuwa 2018, kafin ya koma Al Ain, inda ya lashe gasar UAE Pro League na 2017–18 kuma ya zo na biyu a gasar cin kofin duniya ta FIFA Club World Cup na 2018. Ya zura kwallo daya a wasan daf da na kusa da na karshe a wasan da suka doke Esperance Sportive de Tunis da ci 3-0. [2]A watan Janairun 2019, Elshahat ya shiga Al Ahly.[3] A ranar 4 ga Fabrairu 2021, ya ci wa Al Ahly kwallon nasara a wasan da suka doke Al-Duhail da ci 1–0 a gasar cin kofin kungiyoyin kwallon kafa ta FIFA na 2020 [4]
An kira shi ne zuwa tawagar kasar Masar a watan Agustan 2018, domin karawa da Nijar a wasan neman tikitin shiga gasar AFCON.