Ibrahim Hassan Dankwambo | |||||
---|---|---|---|---|---|
13 ga Yuni, 2023 - District: Gombe North
Mayu 2011 - 29 Mayu 2019 ← Mohammed Danjuma Goje - Muhammad Inuwa Yahaya → District: Gombe North | |||||
Rayuwa | |||||
Haihuwa | Gombe,, 4 ga Afirilu, 1962 (62 shekaru) | ||||
ƙasa | Najeriya | ||||
Ƙabila | Hausawa | ||||
Ƴan uwa | |||||
Abokiyar zama | Adama | ||||
Yara |
view
| ||||
Karatu | |||||
Makaranta |
Jami'ar Ahmadu Bello Jami'ar jahar Lagos | ||||
Harsuna |
Turanci Hausa Pidgin na Najeriya | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | Mai tattala arziki da ɗan siyasa | ||||
Imani | |||||
Jam'iyar siyasa | Peoples Democratic Party |
Ibrahim Hassan Dan kwambo An haife shi a ranar 4 ga watan Afrilu[1] a shekara ta alif da ɗari tara da sittin da biyu, 1962 a unguwar Herwagana dake garin Gombe [2]. Ɗan Najeriya[3] ne, kuma Ɗan siyasa wanda shine tshohon gwamnan Jihar Gombe, dake arewacin Najeriya. Kuma tsohon Accountant General na ƙasa.
Ya kammala karatun digiri ɗin sa na farko a jami'ar Ahmadu Bello dake Zariya a shekarar alif da ɗari tara da tamanin da biyar (1985), inda ya karanci Accounting. Baya ga haka ya samu nasarar kammala karatun sa na Masters a fannin Economic a Jami'ar Legas a shekarar alif dari tara da chasain da huɗu (1994).[5] Sannan ya kammala PhD ɗinsa a fannin Accounting a Jami'ar Igbinedion.[6]
Ya fara aikinsa da Coopers & Lybrand a shekarar alif dari tara da tamanin da biyar (1985), sannan yayi aiki da Babban Bankin Najeriya daga shekara ta 1988 zuwa 1999. A wancan lokacin ne aka sanya shi akaunta janar (Accountant General) na jahar Gombe, ya riƙe wannan matsayi har shekarar dubu biyu da biyar (2005).[7] Ya riƙe wannan ofishin har sanda ya ajiye saboda ya fara neman takarar sa ta kujerar Gwamnan jihar Gombe a watan junairun shekara ta dubu biyu da sha ɗaya (2011).[8]
Ibrahim Dankwambo ya samu nasarar lashe zaben gwamna a jihar Gombe a ranar 26 ga watan Afrilu a shekara dubu biyu da shaɗaya, 2011. Ya lashe zaɓen ne da ƙuri'u 596,481 inda ya mawa Alhaji Abubakar Aliyu na jami'ar APC fintakau wanda yake da ƙuri'u 91,781 da sanata Sa'idu Umar Kumo na jam'iyyar ANPP mai ƙuri'u 84,959.[9]
Yana kan karagar mulki ne, Dankwambo ya rasa mataimakin sa, David Miyims Albashi, wanda ya rasu a ranar 4 ga watan Nuwamba shekarar dubu biyu da goma sha ɗaya (2011) a asibitin Jamani yayin jinya da yakeyi saboda hatsarin mota a ranar 28 a watan Agusta shekarar 2011.[10] A 17 ga watan Disamban shekara ta dubu biyu da shaɗaya, 2011, Dankwambo ya sanya Tha'anda Rubainu a matsayin mataimakin Gwamnan.[11] Bayan sake zaɓen sa na shekarar 2015, Charles Yau shine ya kasance mataimakin Gwamna har ya zuwa ƙarshen tenuwan sa na biyu a shekarar dubu biyu da goma sha tara, 2019.[12] Shine jigon jam'iyyar PDP a jahar Gombe kuma ɗan takarar sanatan Gombe ta arewa a zaɓen da za'a gabatar a shekarar 2023.[13][14]