Ihiagwa | ||||
---|---|---|---|---|
| ||||
Wuri | ||||
| ||||
Yawan mutane | ||||
Harshen gwamnati | Harshen, Ibo |
Ihiagwa gari ne da ke cikin ƙaramar hukumar Owerri ta Yamma a jihar Imo a Najeriya. Garin na da nisan kilomita 12 km (7.5 mi) daga kudu da babban birnin Owerri. Garin kuma ya ƙunshi ƙauyuka takwas: Umuelem, Umuchima, Mboke, Nnkaramochie, Iriamogu, Aku/Umuokwo, Ibuzo da Umuezeawula. An raba Ihiagwa zuwa wasu yankuna biyu masu cin gashin kansu, wato Ihiagwa Ancient Kingdom (Chimelem), wanda ya ƙunshi ƙauyuka biyu: Umuelem da Umuchima; da Dindi-Ihiagwa, wanda ya ƙunshi sauran ƙauyuka shida, duk sassan an yi su ne saboda dalilai na gudanarwa da ci gaba. Kowace al'umma mai cin gashin kanta, sarauta ce da Eze.
Al'ummar Ihiagwa ƴan ƙabilar Igbo ne da ke kudu maso gabashin Najeriya. Mazauna garin sun kai kimanin dubu goma (10,000) kuma cikin sauki akan gane su a cikin mutanen Oratta na Owerri.
Ana kuma kiran mutanen Ihiagwa da Aguzieafors watau masu kiyaye kalanda. Wannan yana nufin a wancan lokacin kafin Biritaniya Ihiagwa ne ke da alhakin kiyaye kalandar al'ummomin da ke kewaye da su kuma suna da alhakin faɗakar da al'ummomin da ke kewaye da ranar bikin bukukuwan; new yam festivals da ma sauran ranaku.
Jami'ar Fasaha ta Tarayya Owerri (FUTO) tana cikin Ihiagwa. Kasuwar Ihiagwa ana kiranta 'Nkwo Ukwu'. Ana amfani da 'Uzi na Aboshi' don nuna Nekede da Ihiagwa saboda 'yan'uwa ne. Makarantar sakandare a Ihiagwa ita ce makarantar sakandaren Ihiagwa da ke Umuchima. Obiwuruotu ita ce ƙungiyar rawa ta mata ta Ihiagwa. Babban addini da ake bi shine Kiristanci. Manyan Coci-coci sun haɗa da cocin Saint John Anglican Ihiagwa, cocin Katolika Ihiagwa da Baptist Church Ihiagwa.
Garuruwan da ke kewaye da Ihiagwa sune Nekede, Eziobodo, Obinze, Naze da Obibiezena. Kogin Otamiri ya ratsa ta cikin Garin.[1]