![]() | ||||
---|---|---|---|---|
![]() | ||||
| ||||
Wuri | ||||
| ||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | |||
Jihohin Najeriya | Jahar Katsina | |||
Labarin ƙasa | ||||
Yawan fili | 892 km² | |||
Bayanan Tuntuɓa | ||||
Kasancewa a yanki na lokaci |
Ingawa Karamar hukuma ce a jihar Katsina a Najeriya . Hedikwatarta tana cikin garin Ingawa.
Garin Ingawa na da yanki na 892 km2 da yawan jama'a 2 a ƙidayar shekarar 2006. Kuma Shugaban Karamar Hukumar a halin yanzu shi ne Alhaji Labaran Magaji da kuma Hakimin hukumar a halin yanzu wato Alhaji Babangida Sule Abubakar Dambo Sarkin Fulani Dambo.
Lambar ofishin tura sakonni na yankin ita ce 823.[1]
Ingawa ta zama karamar hukuma ne a watan Mayun 1989. Ciyaman ne ke jagorantar harkokin karamar hukuma a hukumance. Mafi akasarin mazauna karamar hukumar Hausawa ne da Fulani. Muhimmin aikin su shine noma da kiwo.[2]
Haka kuma, A kan lambobin lasisin ababen hawa, an taƙaita Ingawa a matsayin NGW.[3]
An kafa hukumar ilimi ta Karamar Hukumar Ingawa a shekarar 1989 bayan kafa karamar hukumar Ingawa daga tsohuwar karamar hukumar Kankia.
Wadannan sun zama sakatarorin ilimi daga 1999 zuwa yau.
1. Alhaji Tukur Saude - 1999 – 2002
2. Alhaji Yusuf Bara'u - 2002 - 2012
3. Alhaji Abdu Ibrahim Yandoma - 2012 - Kwanan wata.[4]