Issa Djibrilla | |||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||
Haihuwa | Niamey, 1 ga Janairu, 1996 (29 shekaru) | ||||||||||||||||||||||
ƙasa | Nijar | ||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||
Muƙami ko ƙwarewa | Mai buga tsakiya |
Issa Ibrahim Djibrilla (An haife shi 1 ga Janairun 1996) ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne ɗan ƙasar Nijar wanda ke taka leda a Ankara Keçiörengücü SK ta Turkiyya, da kuma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta kasar Nijar.[1]
A ranar 26 ga Yuli 2021, ƙungiyar Turkiyya ta Keçiörengücü ta sayi Djibrilla kai tsaye.
A ranar 10 ga Oktoba, 2020, Djibrilla ya fara buga wasansa na farko a cikin tawagar ƙasar Nijer a wasan sada zumunci da suka yi da Chadi yaci 2–0.
A ranar 15 ga Nuwamba 2021, ya ci wa Nijar kwallaye 2 na farko a ragar Djibouti a wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin duniya na 2022 da ci 7-2.