Iyanya | |
---|---|
Rayuwa | |
Cikakken suna | Iyanya Onoyom Mbuka |
Haihuwa | Calabar, 31 Oktoba 1986 (38 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Karatu | |
Makaranta | Jami'ar Calabar |
Harsuna |
Ibibio Turanci |
Sana'a | |
Sana'a | mai rubuta waka da mawaƙi |
Muhimman ayyuka |
Kukere (en) Ur Waist (en) Jombolo Sexy Mama (en) |
Artistic movement |
African popular music (en) rhythm and blues (en) |
Jadawalin Kiɗa | Mavin Records |
Imani | |
Addini | Kiristanci |
IMDb | nm6170434 |
Iyanya Onoyom Mbuk (An haife shi a ranar 31 ga watan Oktoban 1986), anfi saninsa da sunansa na waka Iyanya, ɗan Najeriya ne mai mawaki na salon Afropop.
Ya yi suna bayan ya lashe kakar farko na Project Fame West Africa kuma an fi saninsa da wakarsa mai suna " Kukere ".[1][2] Yana da hannu wajen kafa kamfanin wakoki wato Made Men Music Group tare da Ubi Franklin a shekarar 2011. Ya fito da kundinsa na farko na studiyo a shekara ta 2011. Kundin ta hada da wakoki kamar "No time" da "Love Truly". Desire, kundinsa na studio na biyu, ya ƙunshi wakoki guda biyar: "Kukere", " Ur Waist ", "Flavor", " Sexy Mama ", da " Jombolo". Ya lashe lambar yabo ta Artist of the Year a Headies 2013. A cikin watan Oktoban 2016, Iyanya ya sanar a kan shafinsa na Instagram cewa ya sanya hannu kan yarjejeniyar waka tare da Mavin Records.[3] Bayan 'yan watanni kafin, ya sanya hannu kan yarjejeniyar gudanarwa tare da Kamfanin Gudanar da Haikali.[4] Ya fara bayyana aniyarsa ta barin Made Men Music Group a cikin Yuli 2016.[5]
An haifi Iyanya a unguwar Palm a garin Calabar a jihar Cross River.[6] Mahaifiyarsa ita ce shugaban makaranta ce[7] kuma mahaifinsa ma'aikacin gandun daji ne. Iyanya ya bayyana mahaifiyarsa a matsayin mai horo a gida, yayin da mahaifinsa ya kasance mai tausayi. Iyayensa duka sun mutu a shekara ta 2008, kuma ƙanensa ya mutu a lokacin shima.[7] Kakan Iyanya limamin coci ne inda Iyanya ya rera waka a cikin mawakan cocinsa kuma shi ne shugaban mawaka na yara lokacin yana dan shekara biyar.[8]
Mbuk ya kammala karatunsa na firamare da sakandare da jami'a a Calabar. Ya kammala karatunsa a fannun kasuwanci daga Jami'ar Calabar.[9]
Shekara | Taro | Kyauta | Wanda aka ba | Sakamako | Manazarta |
---|---|---|---|---|---|
2014 | City People Entertainment Awards | Gwarzon waka na shekara (Namiji) | Inyanya | Ayyanawa | [10] |
African Muzik Magazine Awards | Fitaccen mawakin Yammacin Afurka | Ayyanawa | [11] | ||
Fitacciyar rawa a bidiyon waka | "Le Kwa Ukwu" | Lashewa | [12] | ||
World Music Awards | Wakar da tafi kowacce dadi a duniya | "Away" | Ayyanawa | [13] | |
"Le Kwa Ukwu" | Ayyanawa | ||||
Bidiyon wakar da tafi kowacce dadi a duniya | Ayyanawa | ||||
Mawakin da yafi kowa iya waka a duniya | Himself | Ayyanawa | |||
Shiri na kai tsaye mafi fice | Ayyanawa | ||||
Fitaccen mai bada nishadi na duniya | Ayyanawa | ||||
2013 | The Headies | Mawakin shekara | Lashewa | [14][15] | |
Gwarzon albam na salon wakar R&B/Pop | Desire | Ayyanawa | |||
Fitaccen albam din shekara | Ayyanawa | ||||
Fitacciyar wakar pop | "Ur Waist" | Ayyanawa | |||
Fitacciyar wakar shekara | Ayyanawa | ||||
Nigeria Music Video Awards (NMVA) | Fitaccen bidiyo mai tsada | "Jombolo" (Iyanya featuring Flavour N'abania) |
Ayyanawa | [16] | |
Fitaccen zamba a waka | N/A | [17] | |||
Fitacciyar amfani da na'urorin gani | "Sexy Mama" (Iyanya featuring Wizkid) |
Ayyanawa | [17] | ||
Soul Train Music Awards | Fitaccen wasan shekara | "Ur Waist" (Iyanya featuring Emma Nyra) |
Ayyanawa | [18] | |
Channel O Music Video Awards | Mawakin da yafi kowa baiwa | "Flavour" | Ayyanawa | [19] | |
Nigeria Entertainment Awards | Fitaccen mawakin Pop/R&B na shekara | Himself | Ayyanawa | [20] | |
Wakar da tafi kowacce dadi na shekara | "Kukere" | Lashewa | [21] | ||
Ghana Music Awards | Gwarzon mawakin Afurka na | Himself | Ayyanawa | [22] | |
City People Entertainment Awards | Mawakin shekara (Namiji) | Ayyanawa | [23] | ||
Wakar da tafi fice | "Kukere" | Ayyanawa | |||
2012 | Nigeria Music Video Awards (NMVA) | Fitaccen wakar zamani (Live Beats choice) | Ayyanawa | [24] | |
The Headies | Fitacciyar wakar Pop | Lashewa | [25] | ||
Wakar shekara | Ayyanawa | [26] |