Wannan mukalar bata da Reference (Manazarta) ko daya, ka taimaka ta hanyar samar da Manazarta daga littafi ko yanar gizo, duba wannan shafin domin samun masaniya akan yanda zaka samar da Reference (Manazarta) a cikin wannan mukalar.
.
Jami'ar Tsaron Nijeriya ita akafi sani da (Nigerian Defence Academy (N.D.A)) dake Kaduna, Najeriya itace makarantar jami'ar dake samar da horo na tsaron kasa daya tilo mallakin sojin Nijeriya. Tsawon shekaru 5 ne akeyi a jami'ar kafin a yaye dalibi, inda shekara hudu anayinsa ne akan karatun ilimi, shekara dayan kuma bayar da horon soja.
Taken jami'ar itace "Amanar kasa da jajircewa", an Samar da makarantar ne a shekara ta alif 1964. Yawan adadin daliban makarantan sunkai kimanin 4,200.
Shafin yanar gizo na jami'ar itace:
www.nda.edu.ng
Akuma n kirkiri jami'ar tun a watan Janairu shekara ta 1964 a matsayin sake gyaran tsohuwar makarantar sojin Kasar Biritaniya wato Royal Military Forces Training College (RMFTC), indkuma a aka canja sunan zuwa makarantar horon soja (Nigerian Military Training College (NMTC)) a ranar samun yancin kai. Jami'ar na koyar da Sojojin Kasa, Sojojin Ruwa, da Sojojin Sama. Aikin farko na jami'ar ta karantar da mutune 62 kacal, kuma yawancin wadanda ke horarwan sojojin kasar indiya ne. Makarantar ta zama na yan Nijeriya kadai a shekara ta 1978, sannan a shekara ta 1981 ta fara koyar da sojojin daga ko'ina a duniya. A kuma shekara ta 1985 ne jami'ar ta fara horar da sojoji da suke bakin aiki da kuma bayar da shaidar digiri na biyu da na uku ga sojojin da wadanda ba sojoji ba.
Babban komanda maici ayanzu shine Major General A. Oyebade.