![]() | |
---|---|
kwaji da secondary school leaving qualification (en) ![]() | |
Bayanai | |
Bangare na |
National Curriculum of Ghana (en) ![]() |
Ƙasa | Ghana da Najeriya |
Ma'aikaci | Kwamitin jarrabawar Yammacin Afirka |
Jarrabawar Manyan Makarantun Sakandare na Yammacin Afirka ( WASSCE ) nau'in jarabawa ce ta tantancewa a Yammacin Afirka. Daliban da suka ci jarrabawar sukan samu takardar shaidar kammala karatunsu na sakandare, Hukumar shirya jarrabawar Afirka ta Yamma (WAEC) ce ke gudanar da jarabawar.[1] Ana ba da ita kawai ga daliban da ke zaune a ƙasashen yammacin Afirka ta Anglophone. Ana kiran takardun shaidar kammala karatun sakandare da ake bayar wa bayan nasarar kammala jarrabawar West African Senior School Certificate (WASSCE).
Jarabawar ta WASSCE ta kunshi gwaji akan mahimman darussa guda huɗu - Turanci, lissafi, kimiyya, nazarin zamantakewa, da sauran zababbun darussa guda uku ko huɗu.[2]
Akwai nau'ikan jarrabawar WASSCE iri biyu:
A karkashin tsarin bada maki na WAEC, ana amfani da haruffa A zuwa F don nuna kyakkyawan sakamako (yayin da lambobi 1-9 ana amfani da su ne kawai don tantance maki). A takaice, don samun A1 a cikin darasi, jarabawar WASSCE a lissafi misali, kuna buƙatar maki aƙalla 75%. Yin haka yana nufin za ku iya samun tambayoyi 75 daidai cikin 100.
A ƙasa akwai bayanai kan tsarin tantancewa, da kuma maki da jami'o'in Najeriya ke amfani da su wajen tantance ɗaliban da za su kammala karatun digiri na farko a shekarar 2021.
Daraja | Daidaiton Lambobi (%) | Maki (%) | Magana |
---|---|---|---|
A1 | 75-100 | 8 | Madalla |
B2 | 70-74 | 7 | Yayi kyau sosai |
B3 | 65-69 | 6 | Yayi kyau |
C4 | 60-64 | 5 | Kiredit |
C5 | 55-59 | 4 | Kiredit |
C6 | 50-54 | 3 | Kiredit |
D7 | 45-49 | 0 | Wuce |
E8 | 40-44 | 0 | Wuce |
F9 | 0-39 | 0 | Kasa |
Ana iya fahimta daga wannan teburi cewa mafi ƙarancin ƙimar wucewa shine C6 (ba tare da la'akari da yabo ba). Ana shawartar dalibai da ke da D7 zuwa ƙasa (musamman a Lissafi da Turanshi) da su sake yin jarrabawar idan suna son ci gaba da karatun manyan makarantu da ake samun ilimin digiri.
Ana shawartar dalibai da cewa za a bukaci su da su cika sharuddan da kowacce jami’a ke buƙata har ma da buƙatun fannukan darasi daban daban na jami’ar da suke son shiga kuma waɗannan buƙatun sun bambanta sosai. Ana iya samun takamaiman bayanai na shiga da ƙa'idodin kora daga jami'o'i ko ƙungiyoyin ƙwararrun wanda abin ya shafa.
Daliban manyan makarantun Sakandare na Najeriya na iya yin jarrabawar WASSCE ko jarabawar National Examination Council (NECO).
Daliban da suka zabi yin karatu a jami’o’in Najeriya, ana bukatar su rubuta jarabawar shiga jami’o’i (Uniified Tertiary Matriculation Examination (UTME)’ wato jarrabawar shiga jami’o’in da hukumar shirya jarabawar shiga jami’o’i ta kasa (JAMB) ke gudanarwa.
Jami'o'in da ke turai wato United Kingdom na iya bukata daga dalibai ƙarin takardar kammala kwas na tushe na shekara ɗaya ko makamancin hakan. Tabbacin ƙwarewa a Turanci na iya zama wajibi.[3]