John Bufton | |||
---|---|---|---|
14 ga Yuli, 2009 - 30 ga Yuni, 2014 District: Wales (en) Election: 2009 European Parliament election (en) | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Llanidloes (en) , 31 ga Augusta, 1962 (62 shekaru) | ||
ƙasa |
Birtaniya Wales | ||
Harshen uwa | Turanci | ||
Karatu | |||
Harsuna | Turanci | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa | ||
Wurin aiki | Strasbourg da City of Brussels (en) | ||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa | UK Independence Party (en) |
John Andreas Bufton (an haifeshi ranar 31 ga watan Agusta 1962) a Llanidloes[1]). tsohon memba ne na Jam'iyyar Independence Party (UKIP) a Majalisar Tarayyar Turai (MEP) dake Wales,[2] daga 2009 zuwa 2014, lokacin da sauka.[3]
Bufton yayi karatu a Makarantar Firamare ta Elan Village da Llandrindod Wells High School,
Ya shiga kasuwancin jigilar dangi kafin ya fara aikin kula da tsofaffi a gida en su tare da ma'aikata.[1]
Bufton ya fara siyasa ne bayan an zabe shi a Majalisar Garin Rhayader a 1987. A cikin 1995, an zaɓe shi zuwa Majalisar gundumar Powys. A cikin Babban Zaɓe na 1997, ya tsaya takarar Jam'iyyar Referendum a mazabar Montgomeryshire.
A shekara ta 2000, ya tsaya takara a matsayin dan takarar UKIP a zaben fidda gwani na Ceredigion, ya zo na biyar da kashi 1.9% na kuri'un da aka kada. Ya kuma tsaya takarar UKIP a Babban Zaben 2005, Zaben Majalisar Welsh na 2007 da zaben Majalisar Karamar Hukumar Powys a shekara ta 2008. [1]
A shekara ta 2009 ne, Bufton ya zama MEP na farko na UKIP don Wales, inda ya ɗauki kujera ta huɗu da ake da ita daga Labour. An nada Bufton don yin aiki a Kwamitin Ci Gaban Yanki, a Majalisar Tarayyar Turai. A watan Mayun 2013, Bufton ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara a zaɓukan Turai na gaba. Nathan Gill ce ta maye gurbinsa.