Johnston Busingye | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Uganda, |
ƙasa | Ruwanda |
Mazauni | Kigali |
Karatu | |
Makaranta |
John F. Kennedy School of Government (en) Jami'ar Makerere |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan siyasa |
Johnston Busingye lauya ne dan kasar Rwanda, hakazalika shine Babban Kwamishinan Ruwanda a Burtaniya na yanzu. [1] A baya, ya yi aiki a matsayin Ministan Shari'a kuma Babban Lauyan Gwamnati, daga shekarar 2013 zuwa 2022. [2]
Yana da digiri na farko a fannin shari'a, wanda ya samu a jami'ar Makerere . Har ila yau, yana da Difloma a fannin Ayyukan Shari'a, wanda Cibiyar Bunkasa Shari'a a birnin Kampala ta ba shi.
Johnston Busingye ya rike mukamai da dama a gwamnatin Rwanda da kuma a bangaren shari'a na kasar Rwanda. daga 2006 zuwa 2013, ya zama shugaban babbar kotun kasar Rwanda. Sauran ayyukan da ya yi a baya, sun haɗa da matsayin mai gabatar da ƙara na ƙasar Rwanda, a matsayin babban sakatare a ma'aikatar shari'a (Minijust), da kuma matsayin babban alkali na kotun shari'a ta gabashin Afirka (EACJ).[ana buƙatar hujja] A matsayinsa na Ministan Shari'a, ya sanar a watan Yuli 2014, shawarar da gwamnatin Rwanda ta yanke, ba zai zama memba naa Kotun Hukunta Manyan Laifuka (ICC) ba.[3]