Joseph Essombe | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Yaounde da Douala, 22 ga Maris, 1988 (36 shekaru) |
ƙasa | Kameru |
Sana'a | |
Sana'a | amateur wrestler (en) |
Nauyi | 55 kg |
Tsayi | 159 cm |
Joseph Émilienne Essombe Tiako (an haife ta a ranar 22 ga watan Maris 1988) 'yar wasan kokawa 'yar Kamaru ce. Ta fafata a gasar women's freestyle 53 kg a gasar Olympics ta bazara ta shekarar 2016, inda Betzabeth Arguello ta fitar da ita a zagaye na 16. [1] [2]
A watan Maris na shekarar alif 2019, ta ci lambar azurfa a gasar women's freestyle 57 kg na mata a gasar kokawa ta Afirka ta shekara ta 2019. A cikin shekarar 2019, ta kuma wakilci Kamaru a gasar cin kofin Afirka ta 2019 kuma ta lashe lambar zinare a gasar kokawa na kilo 53 na mata.
A cikin shekarar 2020, ta lashe lambar zinare a gasar women's freestyle 53 kg a gasar kokawa ta Afirka ta shekarar 2020. [3] Ta samu cancantar shiga gasar Kokawa ta Afirka da Oceania ta shekarar 2021 don wakiltar Kamaru a gasar Olympics ta bazara ta 2020 a Tokyo, Japan. Ta yi asarar lambar tagulla a gasar mata mai nauyin kilo 53. [4]
Ta lashe lambar zinare a gasar da ta yi a gasar kokawa ta Afirka ta shekara ta 2022 da aka gudanar a El Jadida na ƙasar Morocco. [5]