Joyce Msuya | |||
---|---|---|---|
2018 - | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Tanzaniya, 1968 (56/57 shekaru) | ||
ƙasa | Tanzaniya | ||
Mazauni | Nairobi | ||
Karatu | |||
Makaranta |
University of Strathclyde (en) University of Ottawa (en) | ||
Sana'a | |||
Sana'a | microbiologist (en) da environmental scientist (en) | ||
Employers | Majalisar Ɗinkin Duniya |
Joyce Msuya 'yar ƙasar Tanzaniya ce mai nazari a fannin halittu kuma masaniya a fannin kimiyyar muhalli wacce ke aiki a matsayin Mataimakiyar Sakatare-Janar kan Harkokin Jin Daɗin Jama'a da Mataimakiyar Mai Gudanar da Agajin Gaggawa a Ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya mai Kula da Ayyukan Jin kai tun a shekarar 2021. [1] Daga shekarun 2018 zuwa 2021, ta yi aiki a matsayin mataimakiyar Darakta a Hukumar Kula da Muhalli ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNEP) a matakin mataimakiyar Sakatare-Janar.[2]
An haifi Msuya a Tanzaniya, kusan shekarar 1968.[3] Ta sami digiri na farko na Kimiyya a Biochemistry da Immunology daga Jami'ar Strathclyde, Glasgow, Scotland, a shekara ta 1992. Daga baya ta kammala karatun digiri na biyu da digiri na uku a Kimiyyar Halittu da Immunology daga Jami'ar Ottawa, Ontario, Kanada, a shekarar 1996.
Kafin shiga rukunin Bankin Duniya, Msuya ta yi aiki a matsayin Manazarciyar Manufofin Kiwon Lafiya na Duniya tare da Cibiyar Nazarin Duniya ta Liu (yanzu Cibiyar Liu don Al'amuran Duniya ) a Jami'ar British Columbia a Kanada. A baya, ta yi aiki a Tanzaniya a kan ayyuka daban-daban, na masu zaman kansu da na gwamnati.[4]
Msuya ta shiga bankin duniya a shekarar 1998 a matsayin ƙwararriya a fannin lafiya. Ta ci gaba da haɓaka ƙwararru a fannin tattalin arziƙin ci gaba tare da ba da lamuni a fannin kiwon lafiya a lokacin da take aiki a bankin duniya na sake ginawa da bunƙasa (International Bank for Reconstruction and Development). A cikin shekarar 2001, ta zama Mataimakiyar Shugaban Ci gaban tattalin arziki na Bankin Duniya a matsayin mai ba da shawara ga Babban Mataimakin Shugaba da Babban Masanin Tattalin Arziƙi, Farfesa Lord Nicholas Stern.[4] Daga shekarun 2005 zuwa 2011, ta yi aiki a International Finance Corporation, a cikin Sashen Dabarun Ayyuka da Manufacturing, Agribusiness & Services, inda ta kai matsayin Babbar Jami'iyyar Dabarun.
A shekarar 2011, an naɗa Msuya a ofishin Cibiyar Bankin Duniya ta Beijing a matsayin mai kula da yankin Gabashin Asiya da tekun Pasifik, inda ta mai da hankali kan tallafawa ayyukan Bankin a kokarinta na "yaki da talauci da inganta wadatar juna". A cikin watan Afrilu 2014, babban jami'in gudanarwa ya zaɓi Msuya don kafawa da sarrafa ofishin rukunin farko na Bankin Duniya a Jamhuriyar Koriya, tayi aiki na tsawon shekaru uku a matsayin Wakiliyar Bankin Duniya na Musamman ga Jamhuriyar Koriya kuma Shugabar Rukunin Bankin Duniya (WBG) Ofishin da ke Songdo, Incheon, Koriya ta Kudu.[3]
Daga baya Msuya ta zama mai ba da shawara ga Mataimakin Shugaban Bankin Duniya na yankin Gabashin Asiya da Pasifik, wanda ke Washington, DC.[5][6]
Daga shekarun 2018 zuwa 2021, Msuya ta yi aiki a matsayin Mataimakiyar Babban Darakta na Hukumar Kula da Muhalli ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNEP) a matakin Mataimakiyar Sakatare-Janar. Sakatare-Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya António Guterres ne ya naɗa ta a wannan matsayi a ranar 21 ga watan Mayu 2018, na tsawon shekaru 5.[5][7] Ta maye gurbin Ibrahim Thiaw na Mauritania, wanda ya cika wa'adinsa. [5]
Bayan murabus din Erik Solheim a watan Nuwambar 2018, an naɗa Msuya a matsayin Babbar Daraktar na UNEP.[8]
Msuya tana da aure kuma tana da yara biyu.[5]