Judith Uwizeye | |||
---|---|---|---|
31 ga Augusta, 2017 - | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Ruwanda, 20 ga Augusta, 1979 (45 shekaru) | ||
ƙasa | Ruwanda | ||
Mazauni | Kigali | ||
Karatu | |||
Makaranta |
National University of Rwanda (en) University of Groningen (en) | ||
Sana'a | |||
Sana'a | Lauya, ɗan siyasa da Malami |
Judith Uwizeye Lauya ce, Malama kuma 'yar siyasa a ƙasar Rwanda, wacce ta yi aiki a matsayin Minista a ofishin shugaban ƙasa, tun daga ranar 31 ga watan Agusta 2017.[1] Daga watan Yuli 2014 har zuwa Agusta 2017, ta yi aiki a matsayin ministar hidimar jama'a da aiki a majalisar ministocin Rwanda.[2][3]
An haife ta a Ruwanda, a ranar 20 ga watan Agusta 1979.[2] Ta samu digirin digirgir a fannin shari'a a jami'ar ƙasar Rwanda a shekarar 2006. Daga nan ta wuce Jami'ar Groningen da ke ƙasar Netherlands inda ta kammala karatun digiri na biyu a fannin tattalin arziki da kasuwanci na ƙasa da ƙasa.[2][3]
A cikin shekara ta 2006, Uwizeye ta fara koyarwa a tsangayar shari'a a Jami'ar Ƙasa ta Ruwanda ta lokacin, a Huye.[2] Cibiyar ta haɗu da sauran manyan makarantun koyo don zama Jami'ar Ruwanda. A lokacin da aka naɗa ta minista a shekarar 2014, ta kai matsayin mataimakiyar laccara, a fannin tattalin arziki da kasuwanci na ƙasa da ƙasa.[2][3]
Judith Uwizeye ta auri Manase Ntihinyurwa, jami'in kwastam na hukumar tara haraji ta Rwanda, kuma sun haifi yara guda biyu.