Karin Albou | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Neuilly-sur-Seine (en) , 1970 (53/54 shekaru) |
ƙasa | Faransa |
Harshen uwa | Faransanci |
Karatu | |
Harsuna | Faransanci |
Sana'a | |
Sana'a | jarumi, darakta, marubin wasannin kwaykwayo da marubuci |
Mahalarcin
| |
Muhimman ayyuka |
Little Jerusalem (en) The Wedding Song (2008 film) |
IMDb | nm0016900 |
Karin Albou darakta ce mace 'yar kasar Faransa-Algeriya, marubuciya, edita, furodusa kuma yar wasan kwaikwayo.
An haifi Karin Albou a ranar 12 ga watan Maris, shekara ta 1968 [1] acikin Neuilly-sur-Seine zuwa iyayen Yahudawa baƙi 'yan ƙasar Aljeriya. Mahaifiyarta ta kasance tanada shekara sha shida kacal 16 lokacin data haifeta.[2]
A shekara ta 1999 ta koma Tunisia. Bayan shekara guda, ta koma Paris kuma ta fara aikinta a matsayin mai shirya fina-finai da kuma marubuciya.
A matsayinta na yarinya, Albou ta kasance tana shiga cikin rawa da waƙa. Bayan kammala karatun sakandare, Kannan ta cigaba da karatun rawa, amma kuma ta karanci wallafe-wallafe da wasan kwaikwayo, daga bisani ta shiga makarantar fim a birnin Paris. Tayi nazarin rubutun allo amma ta gano cewa tana son zama darekta yayin daukar darasi a École Supérieure de Réalisation Audiovisuelle. Bayan kammala karatun ta, tafito da gajeren fim dinta na farko mai suna Hush! .
Albou tayi fim ɗin ta na farko a cikin shekara ta 2005 mai suna Little Jerusalem, wanda aka fara nuna shi a wajen bikin fina-finai na 2005 Cannes Film Festival a cikin International Critics 'Makon. Duk da kasancewarta fim ɗin farko na Albou, an hana ta shiga gasar Camera d’Or, wanda aka bata kyautar mafi kyawun fim na farko da ta fara fitowa a bikin, saboda abaya ta shirya fim ɗin da akayi don TV.[3]
Acikin shekara ta 2008 Albou ta fitar da fim dinta na biyu Waƙar Aure, wasan kwaikwayo na Holocaust da aka shirya a Tunisiya a cikin shekara ta 1942 wanda ta samu kwarin gwiwa daga wasiƙun da kakarta ta wajen mahaifi ta aika wa mijinta lokacin yaƙi lokacin da aka tura shi sansanin aiki.[4] Fim ɗin ya nuna bukukuwan Yahudawa da yawa amma ya kasa ɗaukar hankalin jama'a, wani abu Albou ta danganta ga yawancin fage na tsiraici a cikin fim ɗin.[5] Fim ɗin Albou na uku 'yar gajerar soyayya ta, wanda ta fito itama a matsayin tauraruwa, an sake shi a cikin shekara ta 2015.[6]
Gadon Karin ta bayyana wasu jigogi da ta zaɓa ta rufe. An taso acikin bangaskiyar Yahudawa, fina-finan Karin sun bincika hargitsi mai ɗorewa na Holocaust[7] - mulkin mallaka na Faransa,[8] sirrinta asali,[9] gudun hijira, ƙaura,[10] da kuma shedan dan ƙasa biyu.[11]
Daraktan ta kuma yi nazari tare da kalubalantar dokokin addini da aure da jigogin soyayya, jima'i da dabi'un iyali.[12] Jigoginta sun haɗa da kawo abubuwan da suka dace na wuraren mata, magance tabarbarewar jima'i a cikin aure da kuma bayyana yadda al'ada ke tasiri akan soyayya.[13] sannan tana kiyaye waɗannan jigogi acikin fina-finanta kuma tana nuna su da salon fim ɗinta na musamman. Salon taya maida hankali ne akan wakilcin mata.[14] A cikin shirin Waƙar Aure, salon fim ɗin yana nuna 'yan madigo, mata, da alaka tsakanin Turawa da Larabawa.
Shekara | Kyauta | Kashi | Fim | Sakamako |
1992 | Cinécinéma[15] | Mafi kyawun Fim na Farko | Chut | Ya ci nasara |
1999 | Clermont - Ferrand Short Film Festival[15] | Mafi Gajerun Gasar Fina-Finan Kasa | Aid El Kebir | Ya ci nasara |
2005 | Bikin Fina-Finan Duniya na Beirut (BIFF)[16] | Mafi kyawun Siffa | Ƙarmar Urushalima | Ya ci nasara |
2005 | Makon Crit a Cannes Film Festival | Mafi kyawun wasan allo | Ƙarmar Urushalima | Ya ci nasara |
2005 | Makon Crit a Cannes Film Festival | Mafi kyawun Siffa | Ƙarmar Urushalima | Wanda aka zaba |
2005 | Deauville Festival | Kyautar Michel d'Ornano [17] | Ƙarmar Urushalima | Ya ci nasara |
2006 | Cesar Awards[15] | Mafi kyawun Fim na Farko | Ƙarmar Urushalima | Wanda aka zaba |
2006 | Cesar Awards[15] | Jami'ar Faransa Cesar | Ƙarmar Urushalima | Wanda aka zaba |
2007 | Cesar Awards[15] | Mafi kyawun Fim na Farko | Ƙarmar Urushalima | Wanda aka zaba |
2007 | Bikin Fim na Yahudawa Berlin[18] | - | Ƙarmar Urushalima | An duba |
2008 | Bikin Daraktocin Matasa na Saint-Jean-De-Luz[15] | Kyautar Jama'a | Wakar Aure | Ya ci nasara |
2008 | Bikin Fim na Montpellier Bahar Rum[15] | Bayani na Musamman na alkali | Wakar Aure | Ya ci nasara |
2009 | Bikin Fim na Yahudawa[18] | - | Wakar Aure | An duba |
2009 | Seattle International Film Festival[18] | - | Wakar Aure | An duba |
2012 | Bikin Fina-finan Hotunan Duniya, Harare[19] | Mafi kyawun Fim | Wakar Aure | Ya ci nasara |
2012 | Bikin Fina-finan Hotunan Duniya, Harare[19] | Mafi kyawun Siffar | Wakar Aure | Ya ci nasara |
2012 | Bikin Fina-finan Hotunan Duniya, Harare[19] | Mafi Darakta | Wakar Aure | Ya ci nasara |
An zabi shirin Waƙar Aure don kyaututtuka 6 a cikin karo na 10 na Bikin HotunanDuniya, Harare.[19]
|url=
(help)
<ref>
tag; no text was provided for refs named auto1